Atiku ko Tinubu: Malamai 1100 Sun Tsaida ‘Dan Takaran Shugaban Kasarsu a Katsina

Atiku ko Tinubu: Malamai 1100 Sun Tsaida ‘Dan Takaran Shugaban Kasarsu a Katsina

  • Malaman addinin Musulunci 1,117 a Katsina sun bayyana goyon bayansu ga sake zaben Bola Ahmed Tinubu
  • Shehunnan sun yi alkawarin wayar da kan mabiyansu da kuma karfafa musu gwiwar zaben shugaban kasa
  • Ibrahim Masari ya nemi malaman su yi amfani da tasirinsu wajen tallata manufofin gwamnatin Tinubu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Katsina - Malaman addinin Musulunci sama da 1,100 a jihar Katsina sun amince su goyi bayan tazarcen Bola Ahmed Tinubu.

Za su mara masa baya domin ya sake lashe zaben shugaban kasa na 2027 a karkashin tikitin Musulmi da Musulmi a APC.

Bola Tinubu da Kashim Shettima
Bola Tinubu da Kashim Shettima wajen kamfe a Kaduna Hoto: Mustapha Samaila Ingawa
Source: Facebook

Malamai 1,117 sun bi Bola Tinubu a Katsina

Jaridar The Sun ta ce baya ga mara masa baya, malaman sun kuma yi alkawarin wayar da kan al'ummominsu game da hakan.

Malaman sun hada da mabiya darikun Qadiriyya da Tijjaniyya da kuma na kungiyar Izala.

Kara karanta wannan

APC ta koma ba Atiku shawara kan abin da ya kamata ya yi wa Tinubu a zaben 2027

Baya ga haka, cikinsu akwai malamai maza, mata da matasa da duk sun bayyana matsayinsu a wajen wani taro da aka yi a jihar.

Malaman sun fito da ra’ayinsu fili a ranar Lahadi 25 ga Oktoba 2026 da suka karbi mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa.

Wanda ya shirya zaman da aka yi da Alhaji Ibrahim Kabir Masari shi ne Dr Aminu Usman, wanda aka fi sani da Abu Ammar a Katsina.

Mai shirya taron, kuma tsohon shugaban Hisbah a Katsina ya ce sun tattauna batun kafin yanke shawarar goyon bayan Tinubu.

Meyasa malaman Katsina suke son Tinubu?

Shahararren malamin ya bayyana cewa matsayinsu na bai daya ne, ba don wata bukata ta kansu ba, sai don ci gaban Najeriya kawai.

Sannan ya kuma bukaci malaman da su wayar da kan jama'a game da wannan matsaya.

The Nation ta ce malaman musuluncin da suke da wannan ra’ayi na goyon bayan tikitin Bola Tinubu/Kashim Shettima sun zarce 1, 117.

Da yake magana, shi kuwa Farfesa Abdulaziz Mashi ya ce sun yanke shawarar ne saboda suna son gwamnati mai-ci ta karasa ayyukanta.

Kara karanta wannan

Saura kwana 80 zabe, an ji gwamnati tana binciken su Peter Obi da shugaban ADC

Suna ganin kyau Tinubu ya kammala manufofi da tsare-tsaren da ya fara shekaru fiye da uku da suka wuce.

Karin hujjojin goyon bayan gwamnatin APC

Farfesan ya nemi malaman su yi nazari kan ayyukan gwamnatin Tinubu, musamman a fannonin ilimi da abubuwan more rayuwa.

Ya kuma ambaci wasu ci gaba da suka samu a jami'o'i, ciki har da kokarin magance matsalolin albashi da walwalar ma'aikata.

Ya ce akwai kalubalen da har yanzu ake fuskanta, amma ya kamata a yaba wa aikin Tinubu.

A cigaban da ya kawo, Mashi ya kawo batun shirin hada Najeriya da Jamhuriyar Nijar ta hanyar layin dogo zuwa Maradi a matsayin.

Shugaban Izala ya yabi shugaba Tinubu

A wajen taron, Shugaban kungiyar Muslim Intellectual Forum, Abdullahi Pakistan, ya yi magana a madadin malaman na Islama.

Farfesa ya koka cewa matsalar tsaro da matsin tattalin arziki na daga cikin manyan kalubalen da Najeriya ta ke fuskanta har gobe.

Sai dai ya ce wasu matsalolin tsaro sun wanzu tun kafin gwamnatin Tinubu ta hau mulki kuma yana ganin ana samun sauki a yanzu.

Kara karanta wannan

Tinubu na Kaduna, El Rufai ya jefa masa tambayoyi 12, ya tuna masa hadisin Manzo

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su ci gaba da addu'ar samun zaman lafiya da inganta tsaro.

Kiran da Ibrahim Masari ya yi wa malaman

Da yake mayar da martani, Masari ya roki limamai da sauran shugabannin addini su sanar da mabiyansu matsayar tasu.

Alhaji Masari yana so malaman su karfafa wa almajiransu tanadar katin zabe su dangwala wa shugaba Tinubu a zaben badi.

An ce Ministan harkokin gidaje, Muttaqa Rabe Darma yana cikin wadanda aka yi taron da su.

Tinubu
Magoya bayan Bola Tinubu a taron yakin zabe a Kaduna Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Mutane sun yi wa shehin Izala rubdugu

An ji labarin cewa ‘yan Facebook sun yi watsa-watsa da Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo da ya zargi sarki da fito-na-fito da shugabanni.

Babban malamin addinin Musuluncin a Najeriya ya shahara wajen tallar jam’iyyar APC musamman a shekarun baya-bayan nan.

Da ya yi kokarin taba sarakuna saboda fada wa masu mulki gaskiya, mutane sun yi masa ca, suna ganin gyara suke so a yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng