Bayan Zargin Trump, Musulmi da Kirista Sun Hadu a Abuja, an Kulla Yarjejeniya
- Fiye da shugabannin addinin Musulunci da Kiristanci 50 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya
- An ƙaddamar da sabuwar ƙungiya da za ta inganta zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, tare da ƙoƙarin dakile kalaman ƙiyayya
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya wakilci Bola Tinubu wajen rattaba hannu, inda ya ce gwamnati na son zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Fiye da shugabannin addinin Musulunci da Kiristanci 50 sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin mabiya addinai a Abuja.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an yi zaman ne domin inganta haɗin kai a Najeriya bayan yawan samun rarrabuwar kawuna.

Source: UGC
An ƙaddamar da wata sabuwar ƙungiya da za ta mayar da hankali kan ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban a faɗin ƙasar, cewar Reuters.
Zargin Trump ya tayar da kura
Al’ummar Najeriya da ta haura miliyan 200 ta kasu kusan daidai tsakanin Musulmi, waɗanda suka fi yawa a arewa, da Kiristoci, waɗanda suka fi yawa a kudanci.
Rarrabuwar addini ta ƙara samun kulawa a watan Nuwambar bara, bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya soki Najeriya tare da yin barazanar ɗaukar matakin soji.
Masu sharhi da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun ce duk da kashe Kiristoci, mafi yawan mutanen da hare-haren suka rutsa da su Musulmai ne.
An cimma yarjejeniyar zaman lafiya
Shugabannin addinai sun bayyana yarjejeniyar a matsayin wani muhimmin sauyi wajen inganta zaman lafiya, tare da rage kalaman da ke haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin al’umma.
Babban Sakataren Ƙungiyar Musulmi ta Duniya, Mohammad Al-Issa, ya ce akwai sha’awar gaske tsakanin ɓangarorin biyu.
Shugabannin Musulmi da Kiristoci daga Najeriya sun bayyana yarjejeniyar a matsayin wani muhimmin mataki wajen samar da zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar.
John Praise Daniel, shugaban Northern Christian Religious Leaders’ Assembly, ya ce yana fatan yarjejeniyar za ta rage kalaman rarrabuwar kawuna daga wasu limamai.
Sakataren-Janar na Jama’atu Nasril Islam, Khalid Abubakar, ya ce yarjejeniyar ba kira ba ce ga mutum ya bar addininsa, sai dai haɗin kai cikin jituwa.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a wajen bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar.
Gwamnonin jihohin arewa uku ma sun halarci taron, wanda aka shirya a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kan addinai.
Yarjejeniyar ta zo ne gabanin zaɓen shugaban ƙasa na watan Janairun 2027, lokacin da ake sa ran addini zai sake taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya.
Jam’iyyar APC mai mulki za ta sake gabatar da tikitin shugaban ƙasa da mataimakinsa Musulmai, kamar yadda ta yi a zaɓen 2023, wanda ya karya tsohuwar al’adar daidaita addinai a tikitin shugaban ƙasa.
Kiristoci sun fusata kan shirin hana wa'azi
Mun ba ku labarin cewa Kungiyar Organisation of African Instituted Churches ta shawarci Shugaba Bola Tinubu kan dokar hana wa'azi.
Ta bukaci shugaban kada ya sanya hannu kan kudirin gyaran dokar FRSC da zai hukunta wa'azi a motocin haya.
Kungiyar ta ce daidaita wa'azi da talla a cikin motocin haya ya saba da kundin tsarin mulki, saboda yana tauye 'yancin addini da fadin albarkacin baki.
Asali: Legit.ng


