Kungiyar Izala Ta Yi Magana kan Bidiyon Ɗan Agaji da Ka Ji Yana Furta Kalaman Tashin Hankali

Kungiyar Izala Ta Yi Magana kan Bidiyon Ɗan Agaji da Ka Ji Yana Furta Kalaman Tashin Hankali

  • Kungiyar Izala ta Najeriya ta yi Allah wadai da bidiyon wani matashi sanye da kayan agajjinta hana fadar kalaman tunzura jama'a
  • Sheikh Bala Lau ya bukaci jami’an tsaro gudanar da bincike kan bidiyon dan agajin, wanda ke ta yada wa a kafafen sada zumunta
  • Mutashin da ya bayyana a bidiyon yana neman a ba su bindigogin AK-47 domin su je Enugu da Joa ranar Lahadi su kai hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS),m da ak fi sani da izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya nesanta kungiyar da wani bidiyon yan agajint da ke yawo a soshiyal midiya.

Bala lau ya yi kakkausar suka kan bidiyin, wanda ya nuna wani matashi sanye da kayan agajin Izala yana furta kalaman tunzura yana neman a ba su bindigogin AK-47 domin su je Enugu ranar Lahadi su kai hari.

Kara karanta wannan

Taohon shugaban APC na Kano ya gamu da hatsari a hanyar dawowa daga wurin kamfen Tinubu

Abdullahi Bala Lau.
Shugaban kungiyar Izala ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau Hoto: JIBWIS Nigeria
Source: Facebook

Kungiyr Izala ta yi Allah wadai tare da nesanta kanta da wannan bidiyo a wata sanarwa da ta wallafa a shafin Facebook.

A martaninsa kan wannan lamari mai tayar da hankali, Sheikh Bala Lau ya yi kira ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), rundunar ’yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro su gudanar da bincike.

Malamin ya nemi a gudanar da bincike domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi ya fuskanci hukunci bisa tanadin doka.

Izala ta nesanta kanta da kalaman

Shugaban ƙungiyar Izala ya bayyana karara cewa JIBWIS ba ta da alaƙa da kalaman tunzura jama’a da aka ji a bidiyon.

Ya jaddada cewa furta kalaman tashin hankali, tsoratarwa da barazana ga kowace al’umma ya saɓa wa ƙa’idoji, koyarwa da manufofin da aka kafa ƙungiyar Izala a kansu.

Ya kuma jaddada cewa sanya kayan agajin Izala ko bayyana tare da mambobinta ba yana nufin cewa mutum yana aiki ne a madadin ƙungiyar ko da izininta ba.

Kara karanta wannan

Ba kamar Tinubu ba, Atiku ya kawo sabon tsari a yakin neman zabensa

Sheikh Bala Lau ya kuma nuna damuwa kan yiwuwar cewa lamarin wani yunƙuri ne da wasu mutane ko wasu da suka shirya domin ɓata sunan Izala da ta daɗe tana ginawa.

Saboda haka, ya buƙaci hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike kan bidiyon, ciki har da gano mutanen da abin ya shafa, alaƙarsu da ƙungiyar da kuma dalilan da suka sa suka aikata hakan.

Taron zaman lafiya na JIBWIS

Shugaban ya tuna cewa a baya-bayan nan JIBWIS ta shirya wani taron ƙasa da ƙasa a Abuja, inda aka haɗa shugabannin Kiristoci, malaman Musulunci daga mazhabobi daban-daban, fitattun mutane da mahalarta daga sassan duniya.

Ya ce babban manufar taron ita ce bunƙasa tattaunawa tsakanin mabiya addinai, fahimtar juna, haƙuri da zaman lafiya.

Sheikh Bala Lau ya tambayi yadda za a danganta ƙungiyar da kalaman da ke kira ga tashin hankali kan ’yan Najeriya, alhali ta daɗe tana amfani da dukiyarta da ƙoƙarinta wajen gina kyakkyawar alaƙa tsakanin mabiya addinai da ƙabila daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262