INEC Ta Tsaida Lokacin da Pantami da Aminu Gwarzo Za Su San Makomar Takararsu
- Wasu masu harin takarar gwamnan 2027 nuna rashin amincewa da INEC ta fitar da sunaye babu su a ciki
- Za a tattauna matakin a taron INEC na gaba, wanda aka tsara gudanarwa ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba 2027
- Sai zuwa Alhamis dinnan ne irinsu Ali Isa Pantami jam’iyyun PDP za su san matsayin takararsu a jihar Gombe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - INEC za ta yanke hukunci kan masu neman takarar gwamna da suka shigar da korafin cewa an cire sunayensu.
Wadanda lamarin zai shafa sun hada da Isa Ali Pantami, Ladi Adebutu, Aminu Abdussalam Gwarzo na PDP da kuma NDC.

Source: Facebook
INEC ta yi waje da wasu 'yan takaran gwamna
A ranar 29 ga Oktoba 2026 za a yi zama game da ’yan siyasar da aka cire sunayensu daga ’yan takara in ji Daily Trust.

Kara karanta wannan
Bayan kama su da laifi, za a rataye jami'an tsaro 3 har lahira a Arewacin Najeriya
Jam’iyyun PDP da NDC sun nuna rashin amincewa da matakin, inda suka nemi hukumar INEC ta sake duba hukuncin.
Hukumar zabe ta kasa ta ce batun ya shafi bin ka’idojin rajistar mambobin jam’iyyun siyasa kafin zaben fitar da gwani.
INEC ta ce matakin ya biyo bayan hukuncin Kotun koli na ranar 24 ga Satumba wanda ya wajabta mika rajistar jam’iyya.
Jam'iyyu sun tura wa hukumar INEC korafi
Jam’iyyun PDP da NDC sun nuna rashin amincewarsu da cire ’yan takararsu, suka aika hukumar INEC korafi na musamman.
Majiyoyi a hukumar zabe ta INEC sun tabbatar wa jaridar cewa za a tattauna korafe-korafen duk ’yan takara a karshen makon nan.
All Africa ta rahoto labarin, tana cewa zuwa ranar Alhamis za a san inda takaransu ta dosa.
Ranar Alhamis INEC za ta yi zama
Wata majiya ta ce an riga an samar da rahoton farko, amma ba za a saki rahoton karshe ba sai bayan karbar duk wani korafi.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Yan bindiga sun rutsa shugaban matasan APC da matarsa a cikin gida
Wasu da suke da masaniya kan batun sun ce sai Alhamis za a zauna saboda shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan yana rangadi.
Ana sa ran farfesan zai ziyarci jihar Gombe a wannan makon, sannan ya dawo ranar Laraba kafin taron da za a shirya kan zancen takara.
Majiyar ta danganta yiwuwar jinkirin duba korafe-korafen da rangadin shiyyoyin da shugaban INEC yake yi gabanin babban zaben 2027.
Korafin da ake kai wa INEC sun ki karewa
An fahimci hukumar ta karbi korafe-korafe da dama kafin cikar wa’adin kwanaki 14 da aka bai wa duka jam’iyyun siyasa a Najeriya.
Wa’adin ya kare ranar Asabar amma hukumar na ci gaba da karbar korafe-korafe har bayan nan.
An yi kokarin jin ta bakin manyan jami’an hukumar INEC irinsu Wilfred Osilama Ifogah da Victoria Eta-Messi, amma dai ba a dace ba.

Source: Facebook
'Yan takaran gwamna da babu sunayensu a INEC
Sheikh Isa Ali Pantami, yana neman kujerar gwamna a jihar Gombe a karkashin jam’iyyar PDP bayan sauya-shekarsa daga APC.

Kara karanta wannan
Nesa ta zo kusa: CDCFIB za ta sake bude shafin ɗaukar ma'aikata a hukumomi 4 a Najeriya
A Benuwai akwai Sebastine Hon wanda ba a ga sunan shi ba c ikin ‘yan takara. Farfesan yana neman gwamna a karkashin SDP.
Akwai Adebutu, dan takarar PDP a jihar Ogun, shi ma INEC ta cire shi a jerin sunayen karshe.
Haka kuma, an yi waje da sunan Aminu Gwarzo, dan takarar jam’iyyar NDC a Kano wanda aka yi tunanin shi zai yaki Abba K. Yusuf.
Asali: Legit.ng