Harry Kane Ya Karya Tarihin Shekaru 25 da Ya Lashe Ballon d’or a 2026
- Harry Kane ya lashe kyautar Ballon d’Or ta 2026, ya zama ɗan Ingila na farko da ya lashe ta tun shekar 2001
- An yi la’akari da cewa dan wasan na kungiyar Bayern Munich ya zura ƙwallaye 73 a kakar wasa ta 2025/2026
- Tauraron na kasar Ingila ya taimaka wa ƙungiyarsa lashe kofunan Bundesliga da DFB-Pokal na Jamus
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
London - Ɗan wasan gaban Bayern Munich da tawagar ƙasar Ingila, Harry Kane, ya lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2026.
‘Dan kwallon ya yi nasarar samun wannan kyauta da ake bayarwa ga fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa a duniya a duk shekara.

Source: Getty Images
Ballon d'or ta fado hannun Harry Kane a 2026
Bayanan da Legit Hausa a shafin Ballon d’or a dandalin X ya tabbatar da nasarar ‘dan kwallon Ingilan a shekarar bana.
Kane ya samu wannan babbar kyauta ne bayan taka rawar gani a kakar wasa ta 2025/2026 da Bayern Munich da kasar Ingila.
‘Dan wasan gaban ya zura ƙwallaye 61 a wasanni 51 da ya buga wa kungiyarsa da ta lashe gasar Bundesliga na kasar Jamus.
Baya ga haka ya ci kofin FA na kasar Jamus wanda aka fi sanin shi da DFB-Pokal.
Kane ya ci kwallaye a gasar kofin duniya
Har ila yau, Kane ya zura ƙwallaye shida a gasar kofin duniya ta 2026, ya jagoranci Ingila zuwa matakin daf da na ƙarshe.
Kasar Argentina ce ta doke Ingila da ci 2-1 a gasar. Kane da ‘yan kasarsa sun iya zuwa na uku bayan nasararsu kan Faransa.
Kasar Ingila ta samu wakilci a Ballon d'or
Kane ya zama ɗan Ingila na farko da ya lashe kyautar cikin shekaru 25, tun bayan Michael Owen ya lashe ta a shekarar 2001.
Haka kuma wannan yana nufin ‘dan wasan shi ne mutumin Ingila na biyar da ya taba samun wannan kyauta a kwallon kafa.
Bayan Owen akwai Stanley Matthews (1956), Bobby Charlton (1966) Kevin Keegan (1978, 1979) da suka gabace shi a tarihi.
Sky Sports ta rahoto shi yana cewa ya gaza magana da ya ji an kira sunan shi a daren Talata.
“Na gode wa duk waɗanda suka zaɓe ni. Ina iya tunanin cewa zaɓen bai kasance mai sauƙi ba. Na gode wa kowa da ya zaɓe ni.”
- Harry Kane
Yadda 'dan kwallon ya yi wa kowa zarra
Baya ga wannan kyauta, shi aka tabbatar a matsayin ‘dan wasan gaban da ya fi kowa yawan kwallaye a kakar da ta wuce.
Kyautar Ballon d’Or na daga cikin manyan lambobin yabo da ake bai wa ’yan wasan ƙwallon ƙafa saboda bajintar da suka nuna.
Ana la’akari da kokarin ‘dan kwallo, nasarar kungiyarsa da kuma da’arsa wajen wasa.
Tsohon ‘dan wasan na Tottenham ya sha gaban Lamine Yamal da Kylian Mbappé da suke buga kwallon kafa a kasar Sifen.
Yamal ya sake zama matashin 'dan wasa da babu irin sa a wannan shekara amma Mbappé bai samu komai ba duk da kokarinsa.
'Yan kwallon duniya a sahun 10 na farko
An saki jerin 'yan kwallon da suka yi zarra a shekarar 2026 a shafin Ballon d'or na yanar gizo. Ga wadanda su ne goman farko.
1. Harry Kane - Bayern Munich & England
2. Kylian Mbappe - Real Madrid & France
3. Lamine Yamal - Barcelona - Spain
4. Rodri - Man City/Barcelona & Spain
5. Lionel Messi - Inter Miami & Argentina
6. Khvicha Kvaratskhelia - PSG & Georgia
7. Ousmane Dembele - PSG & France
8. Erling Haaland - Man City & Norway
9. Michael Olise - Bayern Munich & France
10. Fabian Ruiz - PSG & Spain
Taurarin da suka maida Ballon d'or ruwa

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Jami'an tsaro sun mamaye wuraren da aka liƙa fastoci da allunan tallata Tinubu
Kamar yadda ku ka sani, a tarihi Lionel Messi ne ya fi kowa lashe Ballon d’Or, inda ya lashe ta sau takwas a rayuwarsa.
Cristiano Ronaldo ne na biyu da kyaututtuka biyar, yayin da Cruyff, Platini da Van Basten suka lashe sau uku kowannensu.
Jerin ya nuna bajintar waɗannan fitattun ’yan wasa wajen lashe kyautar da aka fara bada wa shekaru 70 da suka gabata.
Asali: Legit.ng


