Tsohon Hafsan Tsaro Ya Jero Malaman Musulunci 2 da Ya Kamata a Cafke
- Janar Lucky Irabor mai ritaya ya bukaci a hukumomi a Najeriya sun cafke wasu malamai da siyasa a fadin kasar
- Tsohon Shugaban Hafsoshin Tsaro ya goyi bayan gayyatar Sanata Francis Fadahunsi da ’yan sanda suka yi kan kalamansa
- Irabor ya ce hukumomi su dauki mataki kan duk wanda ya yi kalaman tayar da zaune tsaye domin kare zaman lafiya da tsaron Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Shugaban Hafsoshin Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya bukaci a cafke wasu malaman Musulunci.
Irabor ya bukaci hukumomi su kama malaman addinin Musulunci kamar Sani Jingir da Ahmad Gumi.

Source: Twitter
Irabor ya yi wannan kira ne bisa kalaman da ya bayyana a matsayin masu tunzura jama’a, wadanda za su iya kara tabarbarewar matsalar tsaro a Najeriya, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya maida hankali kan samar da ayyuka masu gwaɓi ga matasan Najeriya
Irabor ya bukaci cafke Fadahunsi, malaman Musulunci
Haka kuma, ya goyi bayan gayyatar da ’yan sanda suka yi wa Sanata Francis Fadahunsi kan wata magana mai cike da ce-ce-ku-ce.
Fadahunsi, wanda ke wakiltar mazabar Sanatan Osun Gabas, ya samu gayyatar ’yan sanda ne a ranar Laraba, bayan wani bidiyonsa ya yadu a kafafen sada zumunta.
Ana zargin sanatan da yin magana da za a iya fahimtar cewa yana umartar magoya bayansa su kashe ’yan jam’iyyar Accord da iyalansu gabanin zaben gwamnan Osun.
Sai dai Fadahunsi ya bayyana cewa an gyara ko yanke bidiyon ne domin a ba kalamansa wata ma’ana daban da wadda ya yi nufi.
Irabor ya ce duk wanda ya yi kalaman da za su iya tayar da hankali ya kamata a bincike shi.
Ya ce idan bincike ya tabbatar da cewa kalaman mutum na iya haddasa tashin hankali, hukumomi su dauki matakin da ya dace, ciki har da kama shi.
Irabor ya ce ’yan sanda sun yi abin da ya dace wajen gayyatar Fadahunsi, saboda kalamansa, ko da yake na siyasa ne, sun shafi batun tunzura mutane zuwa tashin hankali.

Source: Facebook
Kalaman Sheikh Jingir da suka jawo maganganu
Game da Sheikh Sani Jingir, Irabor ya ce kalaman malamin na baya-bayan nan ma na iya kara yawan barazanar da Najeriya ke fuskanta.
Sheikh Jingir ya bayyana goyon bayansa ga tikitin Musulmi da Musulmi na jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa, inda ya bukaci Musulmai su yi amfani da karfin kuri’unsu.
Ya yi wannan kira ne yayin wani taron bikin aurar da ma’aurata 1,500 da gwamnatin Kano ta shirya.
Irabor ya kuma ambaci Sheikh Ahmad Gumi, inda ya ce wasu kalaman da malamin ya dade yana yi suna bukatar a kira shi domin ya yi bayani.
Tsohon babban hafsan ya ce kamata ya yi a gayyaci Gumi tare da daukar matakin da ya dace, domin nuna wa jama’a cewa babu wanda ya fi karfin doka.
Ya kara da cewa hukumomi su dauki tsauraran matakai kan kalaman tunzura jama’a domin hana yada maganganun da za su iya lalata zaman lafiya da tsaro.
A cewarsa, daukar irin wadannan matakai zai kuma kara wa jami’an tsaro da sojojin Najeriya kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.
Sheikh Jingir ya yi karin haske kan kalamansa
An ji cewa kalaman da sanannen malamin addinin Musulunci Sani Yahaya Jingir ya yi amfani da su wajen tallata tikitin muslim-muslim na ci gaba da jawo cece-kuce.
Malamin addinin musuluncin ya bayyana cewa yana da 'yancin ya zabi abin da yake so da abin da ya kwanta masa a rai domin ra'ayinsa ne.
Sheikh Jingir ya bayyana cewa ba Shugaba Bola Tinubu yake tallatawa ba, duk da kiran da yake yi na azabi tikitin muslim-muslim.
Asali: Legit.ng

