‘Don Allah, a Bari Mu Sarara’: Kwankwaso Ya ‘Gano’ Shirin Tinubu kan Zaben 2027

‘Don Allah, a Bari Mu Sarara’: Kwankwaso Ya ‘Gano’ Shirin Tinubu kan Zaben 2027

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya kare dimokuraɗiyya, tare da bai wa jam’iyyun adawa dama
  • Kwankwaso ya kuma yi kira da a tabbatar da ’yancin INEC, kotuna da hukumomin tsaro, domin ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya
  • Ya shawarci ’yan Najeriya su guji karɓar kyaututtukan ’yan siyasa yayin zaɓe, su yi amfani da lamirinsu wajen zaɓar shugabannin da suka dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya kare dimokuraɗiyyar Najeriya.

Kwankwaso ya kuma roƙi shugaban ƙasar da ya bai wa jam’iyyun adawa damar gudanar da ayyukansu cikin ’yanci ba tare da tsangwama ba.

Kwankwaso ya shawarci Tinubu kan dimukradiyya
Rabiu Kwankwaso da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Ya yi wannan magana ne a Ibadan, yayin taron masu ruwa da tsaki na Kudu maso Yamma da ƙaddamar da shugabannin ƙungiyar OKAY, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Jagoran Musulmi a duniya ya gana da Bola Tinubu a Abuja

Kwankwaso, wanda Hon. Muktar Umar Zakari ya wakilta, ya ce dole ne a tabbatar da ’yancin hukumomin dimokuraɗiyya kamar INEC, shari’a da jami’an tsaro.

Ya ce mutane sun ji jita-jitar cewa Shugaba Tinubu ba ya son kowa ya shiga zaɓe sai jam’iyyar APC, yana mai roƙonsa ya kyale adawa.

Kwankwaso ya ce Tinubu, wanda ya taɓa kasancewa ɗan adawa kafin ya zama shugaban ƙasa, ya kamata ya bar kyakkyawar tarihi ta hanyar kare dimokuraɗiyya.

“Daga abin da muke gani, mun ji jita-jitar cewa ba ya son kowa ya shiga zaɓe sai jam’iyyar APC, Don haka muna roƙon Shugaban ƙasa ya bar adawa ta kasance. Babu dimokuraɗiyya ba tare da ƙwaƙƙwarar adawa ba.
“Ya bar dimokuraɗiyya ta bunƙasa. Kada ya katse dimokuraɗiyya a wannan karon. Shugabanni da yawa sun zo sun tafi. Ya bar wasu kyawawan abubuwan tunawa. Ya bar tarihin da ’yan Najeriya za su yi alfahari da shi.”

Kara karanta wannan

'Babban kuskure da ƴan Najeriya za su yi idan suka gujewa zaɓen Tinubu a 2027'

Kwankwaso ya shawarci yan Najeriya kan karbar shinkafa a zabe
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana jawabi. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Kwankwaso ya shawarci masu zabe

Tsohon gwamnan ya kuma shawarci masu kaɗa ƙuri’a da kada su bari son rai ko kyaututtuka su rinjayi zaɓinsu, musamman a lokacin babban zaɓen 2027.

Kwankwaso ya ce Najeriya na fuskantar matsalar tsaro da talauci, don haka ya kamata ’yan ƙasa su zaɓi shugabannin da za su kawo sauyi, cewar Daily Post.

“Kada su bari a saye su da son rai kawai ko kyaututtuka. A lokacin zaɓe, ’yan siyasa suna da hanyar rinjayar talakawa. APC ta iya frustrating kowa.
“Ina roƙon ’yan Najeriya su guji shinkafa da sauran kyaututtuka, su zaɓi mutanen da suka dace. Ku saurari lamirinku. Muna cikin matsalar tsaro mai tsanani.”

Ya ce haɗin gwiwar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso shi ne tikitin da zai kawo sauyi, yana mai kira ga ’yan Najeriya su goyi bayansu.

Shugaban ƙasa na ƙungiyar OKAY: A New Nigeria, Hon. Chibuisi Mba, ya ce haɗin gwiwar Obi da Kwankwaso ya fi dacewa da Najeriya.

Kara karanta wannan

Kano ta karyata sanya wasu dattawa a auren gata, ta ba limaman Juma'a umarni

'Babu siyasantar makanta yanzu': Dan majalisar Kano

An ji cewa dan majalisar Kano Sulaiman Mukhari Ishaq Madobi ya ce komawarsu APC ya samo asali ne daga muradin yin abin da ya dace wa jama’a.

Ya shaidawa Legit yadda aka juyar da ra'ayin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya yi yunkurin komawa APC kafin a raba shi da Gwamna.

Hon Mukhari ya ce lokaci ya wuce da ake zabar mutum kawai saboda Jagora, yana mai cewa aikin da aka yi wa jama’a shi ne ya kamata ya zama abin dubawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.