Miyagu daga Kabilar Tibi Sun Hallaka Direban Dangote da Wata Mata a Benue

Miyagu daga Kabilar Tibi Sun Hallaka Direban Dangote da Wata Mata a Benue

  • Wasu da ake zargin ‘yan bindiga masu alaƙa da ƙungiyar Tiv sun yi ta'asa a jihar Benue wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2
  • Dakarun Operation WHIRL STROKE sun gano gawarwakin mutanen biyu a cikin motar Dangote yayin sintirin dare a yankin Igbayima
  • Sojoji sun kwato harsasai 11 da aka harba tare da fara farautar waɗanda ake zargi domin dakile hare-hare a hanyar Kyado–Jootar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ukum, Benue - Majiyoyi sun tabbatar da cewa wasu mutane guda biyu sun rasa rayukansu bayan harin ta'addanci daga miyagu yan kabilar Tibi a Benue.

An gano gawar direban motar Dangote da wata mata a cikin mota yayin da dakarun Operation WHIRL STROKE ke sintirin dare a yankin Igbayima, karamar hukumar Ukum.

Sojoji sun gano gawar direban Dangote da wata mata a Benue
Hafsan sojojin Najeriya, Waidi Shaibu da dakarunsa. Hoto: HQ Nigeran Army.
Source: Facebook

Sojojin Najeriya sun kwato makamai daga miyagu

Kara karanta wannan

An kama dan bindiga makare da Naira da dalolin Amurka yana shirin guduwa

Rahotanni sun nuna cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga masu alaƙa da ƙungiyar Tiv sun kai harin, inda aka kuma kwato harsasai 11 na bindigar 7.62mm, cewar Zagazola Makama.

An kai gawarwakin zuwa ɗakin ajiyar gawa da ke Kyado, yayin da sojoji da ‘yan sanda suka fara bincike tare da neman waɗanda ake zargi.

Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin suna daga cikin masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa a yankin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a gano cikakken bayani game da matar da aka kashe ko yadda ta shiga cikin motar ba.

Dakarun sun kuma kwato harsasai guda 11 na bindigar 7.62mm da aka harba, abin da ke nuna cewa an yi amfani da makamai wajen kai harin.

Ana zargin Tibi sun kashe mata da direban Dangote
Taswirar jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Jami'an tsaro sun bazama nemo waɗanda ake zargi

An kai gawarwakin zuwa ɗakin ajiyar gawa da ke Kyado, sannan aka sanar da ‘yan sanda domin ci gaba da gudanar da bincike.

A halin yanzu, jami’an tsaro suna ci gaba da farautar waɗanda ake zargi da aikata wannan laifi domin hana sake faruwar irin hare-haren a hanyar Kyado zuwa Jootar.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji da yan sanda sun rutsa yan bindiga fiye da 200 ta sama da ƙasa

Harin na na nuni ya kara bayyana irin munin halin da ake ciki, inda motocin haya da sauran masu amfani da hanyar da ke bi ta yankin Kyado–Jootar ke fuskantar barazana, yayin da ake zargin wasu miyagun ’yan kungiyar Tiv da ci gaba da kai wa matafiya da direbobi hari.

Ana sa ran dakarun Operation WHIRL STROKE za su ci gaba da gudanar da sintirin dare da sauran ayyukan tsaro a wannan hanya, domin gano tare da cafke wadanda ke da hannu wajen kai hare-haren, dakile sake aukuwarsu, tare da tabbatar wa mazauna yankin da masu amfani da hanyar cewa ana kare lafiyarsu.

Sojoji sun dakile fadan kabilanci a Plateau

A wani labarin, an ji cewa Sojoji sun dakile wasu mayakan Berom dauke da makamai, wadanda ake zargin sun nufi kai hari kan al’ummomin Fulani a Mangu.

Sojojin sun yi arangama da mayakan a Makera da Kaduno, lamarin da ya tilasta musu janyewa zuwa yankin Jos bayan musayar wuta.

Rundunar ta tura karin dakaru na Special Forces domin taimakawa wajen bin mayakan da suka tsere, tare da hana sake kai hare-hare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.