Wakar Rarara: Ɗan Fim Ya Yi Shagube ga Pantami game da Shiga Siyasa Tsundum

Wakar Rarara: Ɗan Fim Ya Yi Shagube ga Pantami game da Shiga Siyasa Tsundum

  • Ramadan Booth ya soki yadda ake hada maganar addini da siyasa, yana cewa mutane su daina kiran Isa Ali Pantami malamin addini yanzu
  • Jarumin Kannywood ya ce ba ya goyon bayan wakar Dauda Kahutu Rarara, amma ya bukaci jama’a su rarrabe siyasa da addini
  • Ramadan Booth ya ce idan Pantami ya shiga mulki, kundin tsarin mulkin Najeriya ne zai yi amfani da shi, ba Alkur’ani ko Hadisi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Matashin jarumi a masana'antar Kannywood, Ramadan Booth ya tsoma baki game da siyasar Isa Ali Ibrahim Pantami.

Booth yana magana musamman game da wakar da Dauda Kahutu Rarara ya yi da ake alakantawa da Pantami.

Dan fim ya soki Pantami game da neman sassauci a siyasa
Matashi dan wasan fim a Kannywood, Ramadan Booth da Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: Professor Isa Ali Pantami, Ramadan Booth.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Alhamis 13 ga watan Agustan shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Dan Bilki Kwamanda: 'Dalilina na ganawa da Atiku Abubakar'

'A yanzu Pantami dan siyasa ne' - Ramadan Booth

A cikin bidiyon, matashin ya ce abin da mutane ke yi bai kamata ba musamman yadda suke ihu wai an zagi malamin Addinin Musulunci inda ya ce hakan rashin adalci ne.

Ya bayyana cewa shi ba wai goyon bayan mawakin da ya yi hakan yake yi ba, amma mutane su bambance maganar addini da siyasa.

A cewarsa:

"Ni abin nan yana ba ni mamaki, wai sai ka ji mutane suna cewa an zagi malamin addini an yi kaza an yi kaza.
"Don Allah mu dawo hankalinmu, mu yi aiki da idon basira, wani malami aka zaga, ba goyon bayan mawaki nake yi ba.
"Idan kuna maganar an zagi Isa Pantami ne, a baya mai wa'azi ne amma yanzu shi Honorabul Garbati ne."
Dan fim ya yi magana kan shigan Pantami siyasa
Matashin dan wasan fim a masana'antar Kannywood, Ramadan Booth. Hoto: Ramadan Booth.
Source: Facebook

'Jarabawar da Pantami ya samu a rayuwarsa'

Ramadan Booth ya bayyana cewa duk abubuwan da Pantami ya kushe a baya, a yanzu duk Allah ya jarabce shi da su saboda ya zama ishara ga mutane.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari zai bude babin 2023 ya tona abin da ya faru lokacin neman takarar APC

Matashin wanda ya watsar da tafiyar goyon bayan Bola Tinubu karkashin jagorancin Rarara ya ce ko malami ma da kundin tsarin mulki zai yi mulkinsa.

"Don abin da ya fada lokacin da yake wa'azinsa babu wanda Allah bai jarabce shi ba a yanzu.
"Kuna ta malami, malami, shin idan ya hau zai sauya kundin tsarin mulkin Gombe ne ko kuma na Najeriya.
"Ba wai fa da Kur'ani ko hadisi zai yi mulki ba, da wannan kundin tsarin mulkin Najeriya zai yi, mu waye mu rika ware siyasa da addini."

Ramadan Booth

Wakar Rarara: Kwankwaso ya dura kan Isa Pantami

Mun ba ku labarin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce Dauda Kahutu Rarara ya dade yana sukar ’yan siyasa, bai kamata Farfesa Isa Ali Pantami ya fusata ba.

Kwankwaso ya ce Pantami ya bar malanta ya shiga siyasa, don haka bai kamata ya rika tsammanin za a keɓe shi daga sukar ’yan siyasa ba.

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana cewa Rarara ya taba zagin sa, tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje da kuma Sanata Ibrahim Shekarau saboda bambancin siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.