An Tsare Wani Mutum kan Marin Fasto da Ake Zargi da Ɓatanci ga Annabi SAW

An Tsare Wani Mutum kan Marin Fasto da Ake Zargi da Ɓatanci ga Annabi SAW

  • Rundunar ’yan sandan Ghana ta kama wani mutum wanda aka dauka a bidiyo yana marin wani fasto da aka daure da ankwa
  • An zargi Fasto Daniel Junior Yaw Adjei da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad SAW, lamarin da ya jawo kamun nasa
  • ’Yan sanda sun kuma kama limami Masud Abdullah mai shekaru 35, bayan wani bidiyo da ya yi kira da a kai hari kan masu batanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Accra, Ghana - Majiyoyi sun ruwaito cewa Rundunar ’yan sandan Ghana ta cafke wani kan cin zarafin fasot.

An kama Sibamay Zakaria, wanda aka gani a wani bidiyo yana mari wani fasto da aka daure.

An kama wani da ya mari fasto a Ghana
Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama. Hoto: John Mahami.
Source: Facebook

An kama Zakaria ne bayan wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna shi yana bin bayan faston kafin ya mare shi, cewar The Sun.

Kara karanta wannan

Zakaran da Allah Ya nufa da cara: Jariri sabon haihuwa da aka sace ya kubuta

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Alhamis, ta ce Zakaria yana hannun jami’an tsaro kuma yana taimaka wa bincike kan lamarin.

Sanarwar ta ce: “Rundunar ’yan sandan Ghana ta kama wanda ake zargi, Sibamay Zakaria, wanda aka dauka a wani bidiyo da ya yadu yana cin zarafin wani wanda ake zargi.

“Wanda ake zargin yana hannun ’yan sanda yana taimaka wa bincike, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu.

“A halin yanzu, Ofishin Kula da Ka’idojin Aikin ’Yan Sanda yana binciken yanayin da lamarin ya faru, kuma duk wanda aka samu da hannu zai fuskanci matakan ladabtarwa da suka dace.”

An tsare mutum da ya mari fasto a Ghana
Lokacin da aka gano wani dan Ghana yana marin fasto kan zargin batanci. Hoto: Xtrafrica.
Source: Facebook

Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna wani mutum da daga baya aka bayyana sunansa a matsayin Fasto Daniel Junior Yaw Adjei, wanda aka daure da ankwa.

A cikin bidiyon, ana iya ganin Zakaria yana tafiya a bayan faston kafin ya kai masa mari, daga nan, ya tsaya a bayan faston na wani lokaci kafin daga bisani ya bar wurin.

Tun farko, Rundunar ’yan sandan Ghana ta yi Allah-wadai da wannan farmaki, tare da alkawarin gano mutumin da aka gani yana marin faston da kama shi.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Yadda aka kama dan bindiga yana cire kudin fansa a POS

Rundunar ta kuma bayyana cewa za ta gurfanar da wanda aka kama a gaban kotu domin ya fuskanci hukuncin da ya dace.

A ranar Laraba, rundunar ta ce tawagar Cyber Vetting and Enforcement Team ta kama faston, wanda aka fi sani da Apostle Daniel JY Adjei, bayan an kama shi a bidiyo yana yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad SAW.

’Yan sandan sun kuma kama wani limami mai shekaru 35, Masud Abdullah, kan wani bidiyo da aka ga yana kira da a yi amfani da tashin hankali kan mutanen da ke cin mutuncin ko yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad SAW.

Sheikh Mansur ya magantu kan kalaman batanci

Kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto, ya fitar da fayyace matsayar addinin Islama game da batanci ga Fiyayyen halitta.

Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya bayyana abin da ake nufi da 'batanci ga Annabi Muhammad SAW da kuma hukuncin da aka tanada a kan masu kalaman.

Amma ya bayyana cewa duk da hukuncin da aka tanada, hukumomin da shari'a ce ne ke da alhakin zartar da wannan hukunci ba tare da bata lokaci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.