An Fitar da Bidiyon El Rufa'i Ya Sumbaci Matarsa a Harabar Kotu
- Wani bidiyo ya nuna tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai, yana sumbatar matarsa bayan isarsu kotu a Abuja
- Wannan ya faru ne a ranar Litinin, yayin da ake ci gaba da shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan kan zargin kutse ta hanyar sauraron wayar Nuhu Ribadu
- Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta yi watsi da bukatar El-Rufai na neman a soke shari’ar saboda rashin isassun hujjoji, inda ta bukaci ya ya kare kan shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wani bidiyo ya nuna tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yana sumbatar matarsa bayan isarsu Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin.
Wannan lamari ya dauki hankulan jama’a a daidai lokacin da ake ci gaba da shari’ar da gwamnatin tarayya ta shigar a kansa kan zargin kutse ta hanyar sauraron wayar mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Source: Facebook
Abin da ya faru a kotu
Tribune ta wallafa cewa bayyanar El-Rufai a kotun ta zo ne bayan mai shari’a Joyce Abdulmalik ta yi watsi da bukatarsa ta neman kotu ta yanke hukuncin cewa babu isassun hujjoji da za su tilasta masa kare kansa.
Alƙalin ta bayyana cewa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gabatar da isassun hujjoji da suka sa ya zama wajibi El-Rufai ya kare kan shi idan yana so.
El-Rufai, wanda shi ne kaɗai ake tuhuma a shari’ar, ya shigar da bukatar ne bayan DSS ta kammala gabatar da korafinta ta hanyar shaidar mutane biyu.
Lauyoyin sun yi saɓani
Lauyan El-Rufai, Akinyemi Aremu, ya nemi kotu ta yanke hukuncin cewa masu gabatar da ƙara ba su gabatar da hujjojin da suka isa su tilasta wa wanda ake tuhuma ya kare kansa ba.

Source: Facebook
Sai dai lauyan DSS, Oluwole Aladedoye ya yi adawa da bukatar, yana mai cewa masu gabatar da ƙara sun kafa hujjojin farko da suka isa a ci gaba da shari’ar.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun yi amfani da tafiya kamfen Tinubu, sun tafka mummunan ta'adi a Zamfara
Aladedoye ya kuma yi zargin cewa lauyoyin El-Rufa'i ba su yi magana kan hujja ba, wadda masu gabatar da ƙara suka ikirarin El-Rufai dangane da zargin kutse a sadarwar wayar Ribadu yana nan daram.
Tun da farko dai, gwamnatin tarayya ce ta hannun DSS ta shigar da tuhume-tuhume guda biyar a kan tsohon gwamnan.
An yi wa shari’ar rajista da lamba FHC/ABJ/CR/99/2026 a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Ga bidiyon da Channels TV ta wallafa a X:
Akpabio ya sumbaci matarsa
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya sumbaci matarsa, Unoma, a baki bayan Jami’ar Calabar ta karrama ta da digirin girmamawa a fannin kula da harkokin ilimi.
Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da bikin girmama shi ne a matsayin wani ɓangare na bukukuwan cika shekaru 50 da kafuwar jami’ar.
Akpabio ya wallafa saƙon taya matarsa murna, inda ya bayyana ta a matsayin mai ba shi shawara, mai taimaka masa da kuma abokiyar tafiyarsa.
Asali: Legit.ng
