Dan Kwankwasiyya da Ya Rantse da Kur’ani saboda Soyayyar Kwankwaso Ya Koma APC

Dan Kwankwasiyya da Ya Rantse da Kur’ani saboda Soyayyar Kwankwaso Ya Koma APC

  • Daya daga cikin jiga-jigan magoya bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fice daga NDC, inda ya koma jam’iyyar APC
  • Matashin dan siyasar ya ce ya shafe shekaru 29 tare da Kwankwaso, amma ya samu abin da ya kira alkawuran da ba su cika ba
  • Dan siyasar ya bayyana cewa zai goyi bayan Shugaba Bola Tinubu domin sake zaɓensa a 2027, bayan ya ajiye takardar murabus daga NDC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Wani dan Kwankwasiyya, Kabiru Adamu Abdullahi da ya kasance tsohon aminin Rabiu Musa Kwankwaso ya bar tafiyarsa.

Kabiru ya bar bangaren ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, inda ya sauya sheka zuwa APC.

Dan Kwankwasiyya ya koma APC
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Kabiru Adamu Abdullahi. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Kabiru Adamu Abdullahi.
Source: Facebook

Ya aike da takardar murabus ga shugaban jam’iyyar na Kofar Ruwa Ward da ke ƙaramar hukumar Dala, inda ya bayyana dalilan yanke shawarar, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Don Allah, a bari mu sarara': Kwankwaso ya 'gano' shirin Tinubu kan zaben 2027

Wani dan Kwankwasiyya ya gana da Abba

Wannan na zuwa ne bayan samun yawan sauya sheka daga bangaren Kwankwasiyya a Kano zuwa tsagin Abba Kabir yayin da ake shirin gudanar da zaben 2027.

Shugaban ƙungiyar Kwankwasiyya ta ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano, Alhaji Abdulaziz Gidanruwa, ya ziyarci Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Gidanruwa, wanda ake bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu ɗaukar nauyin NDC da ƙungiyar Kwankwasiyya a Nassarawa.

Ziyarar ta ƙara haifar da hasashen sauye-sauyen siyasa a Kano yayin da jam'iyyu ke fara shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Masoyin Kwankwaso ya watsar da shi zuwa APC
Kabiru Adamu Abdullahi da Sanata Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

Kabiru ya rantse da Kur'ani kan Kwankwaso

Kabiru, wanda a baya ya rantse da Alƙur’ani domin tabbatar da amincinsa ga Kwankwaso bayan rabuwa da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga NDC.

Ya ce rashin gamsuwa da abin da ya bayyana a matsayin “failed promises” a cikin NDC ne ya sa ya ɗauki wannan mataki.

Kara karanta wannan

Shugaba a Kwankwasiyya ya gana da Abba Kabir, yana shirin shiga APC

Abdullahi ya kuma bayyana cewa yanzu zai mara wa Shugaba Bola Tinubu baya domin sake zaɓensa a ƙarƙashin jam’iyyar APC a shekarar 2027.

Ya ce:

“Na shafe shekaru 29 tare da Kwankwaso, amma abin da na amfana da shi kawai shi ne alkawuran da ba su cika ba. Zan koma inda za a fi girmama ni.”

A cikin takardar murabus ɗin, ɗan siyasar ya gode wa NDC bisa damar da ta ba shi ta yi wa jam’iyyar hidima, amma ya tabbatar da ficewarsa daga cikinta nan take.

Wannan murabus din da matashin ya yi ya kara sanya shakku kan siyasar amana a Najeriya duba da shekarun da suka shafe tare da a Kwankwasiyya.

Kwankwaso ya ba Tinubu kan zaben 2027

A baya, mun ba ku labarin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya kare dimokuraɗiyya, tare da bai wa jam’iyyun adawa dama.

Kwankwaso ya kuma yi kira da a tabbatar da ’yancin INEC, kotuna da hukumomin tsaro, domin ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya.

Ya shawarci ’yan Najeriya su guji karɓar kyaututtukan ’yan siyasa yayin zaɓe, su yi amfani da lamirinsu wajen zaɓar shugabannin da suka dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.