Sojojin Amurka Sun Rasa Rayukansu bayan Faɗuwar Jirgin Saman Yaƙi

Sojojin Amurka Sun Rasa Rayukansu bayan Faɗuwar Jirgin Saman Yaƙi

  • Sojojin Amurka sun mutu bayan wani jirgin sama mai saukar ungulu kirar Apache na sojojin Amurka ya yi hatsari
  • Jirgin mai saukar ungulu na AH-64 Apache, wanda ke sansanin Fort Hood, ya fado cikin wani fili a Salado, ba tare da buga gidaje ba
  • Hatsarin ya kuma haddasa gobarar daji, yayin da hukumomi suka fara bincike kan musabbabin hatsarin tare da sanar da sunayensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Texas, US - Sojoji biyu na Amurka sun mutu bayan wani jirgin sama mai saukar ungulu kirar Apache na rundunar sojin Amurka ya yi hatsari a Salado, Texas.

Ofishin Sheriff na Bell County ya ce mutane biyu ne ke cikin jirgin, kuma an tabbatar da mutuwarsu a wurin da hatsarin ya faru da misalin karfe 2:30 na rana agogon yankin.

Kara karanta wannan

Duka bayanan da suka fito daga juyin mulkin da aka yi yunkurin yi wa Tinubu

Jirgin sojojin Amurka ya fadi
Shugaban Amurka, Donald Trump jim kadan bayan jawabi ga 'yan majalisar Republican a Doral, Florida. Hoto: Roberto Schmidt.
Source: Getty Images

Mai magana da yawun ofishin, Bill Coleman, ya ce jirgin ya fado cikin wani fili, kuma bai buga wani gida ko wata gini ba, cewar CBS News.

Ana dakon bayyana sunayen sojojin

Sojojin Amurka sun ce za su bayyana sunayen wadanda suka mutu bayan awanni 24 da sanar da iyalansu.

“Za ka iya gane cewa wannan hatsari ne mai muni."

- in ji Coleman.

Lamarin ya tayar da hankula tare da saka fargaba game da jiragen yaki da ke samun matsaloli waɗanda ke jawo rasa rayuka da dukiyoyi.

Birgediya Janar Ethan Diven, mukaddashin kwamandan Fort Hood, ya tabbatar da cewa jirgin mai saukar ungulu kirar AH-64 Apache yana karkashin sansanin Fort Hood.

Ya ce:

“Babban abin da muka fi mayar da hankali a kai yanzu shi ne tabbatar da tsaron wurin da kuma tallafa wa jami’an da ke gudanar da martanin farko.
" Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga ma’aikatan jirgin da iyalansu, yayin da muke jiran karin bayani.”

Kara karanta wannan

Da gaske ne: Trump ya tabbatar da fargabar harin Iran, ya yi basaja a cikin jirgi

Sojojin Amurka sun mutu a hatsarin jirgi
Jirgi yakin Amurka a sararin samaniya Hoto: Jalaa Marey.
Source: Getty Images

Ana ci gaba da bincike kan hatsarin jirgi

Ya zuwa lokacin rahoton, rundunar sojin Amurka ba ta bayyana musabbabin hatsarin ko sunayen wadanda suka mutu ba.

Coleman ya kuma ce hatsarin ya haddasa wata gobara a yankin, wadda har zuwa misalin karfe 3:30 na rana take ci ba tare da an shawo kanta ba, cewar BBC.

An ga wani jirgin dakon ruwa yana zubar da sinadarin kashe gobara a wani fili da ke kudu maso yammacin Salado, bayan hatsarin jirgin sojan ya haddasa gobarar ciyawa.

Sansanin Fort Hood yana kusa da Killeen, Texas, a arewa maso yammacin Salado, kuma yana da tazarar kusan mil 70 daga Austin.

Trump ya sauya jirgi saboda tsoron Iran

Mun ba ku labarin cewa shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun sauya jirginsa a asirce saboda tsaro.

An kawo rahoto cewa hukumomin Amurka sun gano sahihiyar barazanar Iran ta kai wa jirgin shugaban hari, lamarin da ya sa aka mayar da shi wani jirgin soja.

Trump ya ce bai nemi cikakken bayani kan barazanar ba, yana mai cewa yana fuskantar barazana da dama wanda ba zai iya misalta su ba tun bayan hawansa mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.