Taohon Shugaban APC na Kano Ya Gamu da Hatsari a Hanyar Dawowa daga Wurin Kamfen Tinubu

Taohon Shugaban APC na Kano Ya Gamu da Hatsari a Hanyar Dawowa daga Wurin Kamfen Tinubu

  • Tsohon shugaban APC a Kano, Abdullahi Abbas, ya tsallake rijiya da baya a wani haɗarin mota yayin dawowa daga taron kamfen ɗin Tinubu a Kaduna
  • Rahotanni sun nuna cewa motar da yake ciki ta lalace gaba ɗaya, amma babu wanda ya ji rauni daga cikin wadanda ke ciki
  • Shugabannin jam'iyyar APC sun kai masa ziyara a gidansa domin yi masa jaje kan abin da ya faru da addu'ar neman kariya a gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Tsohon shigaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya gamu da hatsarin mota a hanyar komawa gida bayan halartar taron kaddamar da yakin neman zaben APC a Kano.

Bayanai daga makusantan Alhaji Abdullahi Abbas, sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka bayyana cewa ya tsallake rijiya da baya a wani haɗarin mota da ya rutsa da shi.

Kara karanta wannan

Wike ya faɗi abin da zai hana Obi zama shugaban ƙasa, ya tuna mummunan halinsa 1

Abdullahi Abbas.
Taohon shugaban Ajam'iyyar PC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas Hoto: Abdullahi Abbas
Source: Facebook

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Abbas ya halarci taron kaddamar da yakin neman sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya gudana ranar Asabar 24 ga watan Oktoba, 2026.

Tsohon shugaban APC ya yi hatsari

Makusantan babban jigon APC sun ce hatsarin ya faru ne yayin da yake hanyar komawa gida a jihar Kano daga Kaduna.

Sun bayyana cewa motar da Abdullahi Abbas yake ciki ta lalace gaba ɗaya a hatsarin, amma shi da sauran mutanen da ke cikinta ba su samu ko ƙwarzane ba.

Sanarwar da Abba Rabi’u Gwarzo, jami’in yaɗa labarai na shugaban APC na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya fitar ta ce:

“Tabbas, Alhaji Abdullahi Abbas ya yi hatsari yayin dawowarsa daga taron APC a Jihar Kaduna, kamar yadda gidajen jaridu ke yaɗawa. Amma cikin ikon Allah, babu wanda ya samu ko ƙwarzane a cikinsu, har da shi kansa.”

An fara zuwa jajantawa Abdullahi Abbas

Kara karanta wannan

Tinubu na Kaduna, El Rufai ya jefa masa tambayoyi 12, ya tuna masa hadisin Manzo

Ya bayyana cewa shugaban jam’iyyar APC na Kano, tare da sauran ’yan uwa da abokan arziki, sun ziyarci Abdullahi Abbas a gidansa da ke Charanchi ranar Lahadi, 25 ga Oktoba, 2026, domin yi masa jaje.

A ranar Asabar, 24 ga Oktoba, aka ƙaddamar da yaƙin neman sake zaɓen Shugaba Tinubu a Jihar Kaduna.

Ana kallon taron a matsayin mai matuƙar muhimmanci, ganin cewa shugaban ƙasar ya riga ya bayyana cewa ba zai iya ziyartar dukkan jihohin Najeriya domin yaƙin neman sake zaɓensa ba.

Duk da haka, masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa zai ziyarci Kaduna da wasu jihohi 11 ne kawai daga cikin jihohi 36 na ƙasar da Babban Birnin Tarayya.

Magoya bayan APC sun yi hatsari

A wani labarin, kun ji cewa wasu magoya bayan APC sun yi hatsarin mota a Lafia, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gangamin taron da aka shirya saboda Tinubu.

Lamarin ya faru ne yayin da suke shirin zuwa Nasarawa, domin halartar babban gangamin yankin Arewa ta Tsakiya na nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu .

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262