Ba Tinubu ba ne Matsalar, an 'Gano' Abin da Ya Hana Ruwa Gudu a Najeriya
- Mawaki a Najeriya, Femi Kuti ya ce Shugaba Bola Tinubu ba shi ne babbar matsalar Najeriya ba kamar yadda wasu suke tunani a kasar
- Kuti ya ce tsarin shari’ar Najeriya ya kamata ya kasance mai ƙarfi, har ya hana mutanen da ake zargi da manyan laifuka tsayawa takarar shugabanci
- Femi Kuti ya ce cin hanci ya yi katutu a Najeriya, yana shafar cibiyoyi da dama tare da rage wa matasa kwarin gwiwar makomar ƙasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Mawakin Afrobeat da aka taba tantance shi a Grammy, Femi Kuti, ya yi magana game da matsalolin Najeriya.
Kuti ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi ne babbar matsalar Najeriya ba kamar yadda wasu suke zato.

Source: Instagram
Kuti ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin GoodNews Naija podcast, inda ya yi magana kan shugabanci.
Abin da ke hana ruwa gudu a Najeriya
Ya ce cin hanci da rashawa da ke cikin tsarin hukumomin ƙasar shi ne babban ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.
Kuti ya tattauna batutuwan cin hanci da rashawa, shugabanci da kuma rawar da hukumomin gwamnati ke takawa wajen tafiyar da Najeriya.
A cewarsa, tsarin shari’ar ƙasar ya kamata ya kasance mai ƙarfi har ya hana duk wanda ke fuskantar manyan zarge-zarge tsayawa takarar mukamin gwamnati.
Ya ce:
“Shin kuna ganin Tinubu ne matsalar? Tsarin shari’ar da bai hana shi kaiwa wannan matsayi tun farko ba shi ma matsala ne.
“Idan duk zarge-zargen da ake masa gaskiya ne, ta yaya ya samu damar tsayawa takara? Idan muna da mutanen kirki, hakan ba zai faru ba."
Illar da cin hanci, rashawa ke yiwa Najeriya
Femi Kuti ya ce cin hanci da rashawa ya yi katutu a Najeriya, kuma yana shafar fannoni daban-daban na rayuwar al’ummar ƙasar baki ɗaya.
Ya ce mutane da aka damƙa wa shugabancin hukumomi daban-daban a Najeriya galibi suna cikin rukunin masu hannu da shuni na siyasa da tattalin arziki.
Mawakin ya ƙara da cewa cin hanci da rashawa da ke cikin tsarin gwamnati ya taimaka wajen ƙara takaicin matasan Najeriya da kuma raunana musu fata.
A cewarsa, wannan yanayi na iya rage wa matasa kwarin gwiwar cewa Najeriya za ta samu makoma mai kyau yayin da dama daga yan kasar suke fatan ganin an samu sauyi a yanayin shugabanci.
Tsohon hadimin Tinubu ya dura kansa
Mun ba ku labarin cewa Hakeem Baba-Ahmed ya ce ’Yan Najeriya za su kori APC a 2027 idan aka gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.
Shugaban PRP ya ce kada APC ta ji tsoron jam’iyyun adawa, domin ’yan Najeriya ne ke da ikon yanke hukuncin zabe ba wai azzaluman daga shugabanni ba.
Hakeem Baba-Ahmed ya gargadi ’yan adawa kan kawancen da ba shi da cikakken shirin tafiyar da Najeriya gaba inda ya bukaci jajircewa daga gare su.
Asali: Legit.ng

