'Ubangiji ne Ya Turo Ni Gare Ku saboda Shi': Minista Ya Faɗi Alherin Tinubu
- Ministan Ayyuka, Dave Umahi, ya bayyana ayyukan alheri da shugaba Bola Tinubu ke yi a fadin Najeriya wanda ya cancanci tazarce
- Umahi ya ce gwamnatin Tinubu na mai da hankali kan inganta ababen more rayuwa a yankin, musamman manyan tituna
- Ministan ya danganta rawar da yake takawa da samun ayyukan raya kasa ga yankin, yana cewa Ubangiji ne ya turo shi ya faɗi gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abakaliki, Umahi - Ministan Ayyuka, Dave Umahi, ya ce Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya aikata ayyukan alheri ga al'ummar Najeriya baki daya.
Umahi ya ce Tinubu ya na da kyakkyawar niyya ga al’ummar Kudu maso Gabas, inda ya buƙaci mazauna yankin su guji kallon ayyukan gwamnatin tarayya da son zuciya.

Source: Facebook
Umahi ya bayyana hakan ne a wasu kalaman da aka yaɗa a kafafen sada zumunta inda ya yi ƙarin haske kan ayyukan shugaban a Kudu maso Gabas, cewar Vanguard.
Umahi ya yaba salon mulkin Tinubu
Ministan ya yi magana kan ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na aiwatar da ayyukan more rayuwa da kuma shigar da Kudu maso Gabas cikin shirye-shiryen ci gaban ƙasa.
A cewar ministan, Kudu maso Gabas na samun kulawa a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, wadda ya ce ta himmatu wajen magance wasu matsalolin ababen more rayuwa da suka daɗe suna addabar yankin.
Umahi ya ce:
“Kudu maso Gabas, a karon farko ana tunawa da mu…, saboda wani lokaci nakan ce ku saurara, mutanenmu kada su kasance masu son zuciya.
"Shi ya sa suke zage ni, kuma ina jin daɗin zagin, domin gobe za su gano cewa, kun sani, ubangiji ne ya aiko ni a irin wannan lokaci domin in gaya muku gaskiya.
" Shugaban ƙasa yana da kyakkyawar niyyar haɗa mutanen Kudu maso Gabas cikin ci gaban ƙasa, kuma dole in kasance mai gaskiya a gare ku.”

Source: Twitter
Ayyukan Tinubu a Kudu maso Gabas
Umahi ya kuma ce kasancewarsa a Majalisar Zartarwa ta Tarayya ya taimaka wajen ganin yankin ya samu wasu ayyukan more rayuwa, yana mai bayyana aiwatar da ayyukan a matsayin wani yunƙuri na gyara abin da ya kira kura-kuran da aka yi wa Kudu maso Gabas a baya.
Ya ce:
“Da ba ni ne minista daga Kudu maso Gabas ba, da ba za mu iya samun ayyukan da muka samu ba. Don haka, wannan niyyar Shugaban ƙasa ce. Ku je ku gyara kura-kuran da aka yi wa Kudu maso Gabas.”
Ministan ya kuma yi amfani da misalan Littafi Mai Tsarki wajen jaddada muhimmancin mutane su bayar da gudunmawa wajen ci gaban yankinsu tare da amfani da damar da suke da ita.
Kalaman Umahi sun zo ne yayin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da jaddada cewa bunƙasa ababen more rayuwa na daga cikin manyan manufofinta na haɗa sassan ƙasar da sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki, cewar Punch.
Habila: Abin da Tinubu ya fadawa minista
Kun ji cewa Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya yi masa magana bayan an nemi ya kore shi saboda mutuwar wata ma'aikaciya.
David Umahi ya ce wasu sun mayar da mutuwar wata ma’aikaciyarsa, Mary Habila, batun siyasa tare da neman a tsige shi.
Ministan bai yi bayani kan binciken da ake gudanarwa kan mutuwar Habila ba, amma ya ce zai ci gaba da sauke nauyin da ke kansa.
Asali: Legit.ng


