Ana Zargin Dan Sanda Ya Bude Wuta a wajen Maulidi, Ya Yi Kisan Kai
- Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta buƙaci hukumomin Najeriya su gudanar da bincike kan kisan wani matashi mai shekaru 15 zuwa 16 a jihar Borno
- An kashe matashin mai suna Umar Muhammad, wanda aka fi sani da Gajiye, a wani taron Maulidi da aka gudanar a Banki, ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno
- Amnesty ta ce ya kamata a gudanar da bincike cikin gaggawa tare da tabbatar da cewa duk jami’an ’yan sandan da ke da hannu a kisan sun fuskanci shari’a ta gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su gudanar da bincike kan kisan wani matashi a yayin taron Maulidi a jihar Borno.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun yi amfani da tafiya kamfen Tinubu, sun tafka mummunan ta'adi a Zamfara
An kashe Umar Muhammad, wanda aka fi sani da Gajiye, mai shekaru 15 zuwa 16, a Banki, ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno, inda ake zargin wani jami’in ’yan sanda mai muƙamin Superintendent of Police ne ya harbe shi.

Source: Facebook
Amnesty International ta bayyana a Facebook cewa ya kamata a gudanar da bincike kan lamarin cikin gaggawa tare da tabbatar da cewa duk jami’an ’yan sandan da abin ya shafa sun fuskanci shari’a.
Yadda aka kashe matashin
Shaidun gani da ido sun cewa wani jami’in ’yan sanda mai muƙamin Superintendent, tare da tawagarsa, sun je wurin taron Maulidi domin nuna rashin jin daɗinsu kan abin da suka bayyana a matsayin hayaniya mai yawa da ke fitowa daga lasifikokin taron.
Amnesty ta wallafa cewa bayan haka, masu shirya taron sun kashe lasifikokin domin bin umarnin ’yan sandan.
Sai dai, bayan ɗan lokaci, ana zargin jami’in ya dawo wurin tare da wasu ’yan sanda, inda suka kori mutane tare da fara harbe-harbe.
Rahoton ya bayyana cewa an harbi Umar Muhammad, wanda ya mutu a wurin, inda aka bar shi cikin jini.

Source: Original
Amnesty ta bukaci bincike
Amnesty International ta buƙaci rundunar ’yan sandan Najeriya ta gudanar da bincike na gaskiya ba tare da nuna son kai ba, tare da tabbatar da cewa duk jami’an da aka samu da hannu a kisan sun fuskanci shari’a cikin adalci.
Ƙungiyar ta bayyana cewa abin da ya faru da Umar Muhammad ya sake bayyana wani yanayi na take haƙƙin bil’adama, inda ake zargin masu aikata irin waɗannan laifuka ba sa fuskantar hukunci.
Ta kuma nuna damuwa kan yadda rundunar ’yan sandan Najeriya, wadda aka kafa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, ke fuskantar zarge-zargen take haƙƙin bil’adama ba tare da an hukunta masu aikata laifukan ba.
An saki 'yan Tinubu Must Go
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata kotu ta bayar da belin wasu mutane biyar da aka kama a jihar Borno bisa zargin sanya rigunan da aka rubuta “Tinubu Must Go”.
Shugaban matasan jam’iyyar ADC, Balarabe Rufai, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, kwanaki bayan da rundunar ’yan sandan jihar Borno ta kama mutanen tare da gurfanar da su a gaban kotu.
An kama mutanen, waɗanda suka haɗa da Baba Aji Gremami, Mustapha Abba Yemen, Abbacha Mohammed Ali, Adam Umar Gubio da Abdulhamid Mohammed, a Maiduguri ranar 25 ga Satumba.
Asali: Legit.ng
