IPOB: Kungiyar 'Yan Ta'adda Ta Yi Magana kan Alaka da APC a 2027
- Ƙungiyar IPOB ta umarci magoya bayanta da su kaurace wa duk wani abu da ya shafi jam’iyyar APC, tana zargin gwamnati da kawo cikas ga ɗaukaka ƙarar Nnamdi Kanu
- A bayanin da ta yi, kungiyar ta ce umarnin kauracewa APC shi ne mataki na farko kafin ta fara kira ga cikakken kaurace wa zaɓen 2027
- IPOB ta kuma yi zargin cewa an ɓatar da fayil ɗin ƙarar Kanu, yayin da ta yi watsi da saƙon sauti da ke cewa an dawo da dokar zaman gida a ranar Litinin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ƙungiyar IPOB ta umarci magoya bayanta da su kaurace wa duk wani abu da ya shafi jam’iyyar APC, tana zargin gwamnatin tarayya da hana sauraron ɗaukaka ƙarar jagoranta da ke tsare, Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan
Da gaske an fitar da Naira tiriliyan 2.3 don ƙaddamar da kamfen APC a Kaduna? Gaskiya ta fito
A cikin jawabin mako-mako da ƙungiyar ta fitar ranar Lahadi, hukumar gudanarwarta ta ƙasa (DOS), ƙarƙashin jagorancin Mazi Chris Nwaogu, ta ce umarnin zai fara aiki nan take.

Source: Twitter
The Sun ta wallafa cewa kungiyar ta bayyana matakin a matsayin farkon wani shiri na janye goyon bayan siyasa a matakai, kafin ta yi kira ga cikakken kaurace wa babban zaɓen 2027.
IPOB ta kaurace wa APC
Nwaogu ya buƙaci magoya bayan ƙungiyar da su daina halartar tarukan yaƙin neman zaɓen APC, ɗaukar tutocin jam’iyyar ko kare gwamnonin da ke ƙarƙashinta.
Ya kuma yi zargin cewa duk wani ɗan kabilar Igbo da ya yi yaƙin neman zaɓen APC yana aiki ne a matsayin maƙiyin al’ummarsa.
Sai dai ƙungiyar ba ta bayyana yadda za ta tabbatar da aiwatar da wannan umarni ba.
IPOB ta ce matakin na daga cikin shirin da take bi a hankali na janye goyon bayanta ga harkokin siyasar APC, wanda za a iya faɗaɗa shi zuwa kaurace wa zaɓen 2027.
Magana kan tsare Kanu
Rahoton Daily Post ya nuna cewa IPOB ta zargi wasu ɓangarori na tsarin shari’a da kawo cikas ga shari’o’in da suka shafi Kanu.
Ta yi iƙirarin cewa a zaman kotu da aka gudanar mako biyu da suka gabata, alƙalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya bayyana cewa an ɓatar da fayil ɗin ƙarar da Kanu ya shigar kan take masa haƙƙoƙinsa na ɗan Adam.
Ƙarar ta shafi zargin tsare Kanu na tsawon wata14 bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta sallame shi a ranar 13 ga Oktoba, 2022.
Ƙungiyar ta kuma ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta sanya ranar sauraron ƙarar da Kanu ya shigar kan hukuncin da aka yanke masa a ranar 20 ga Nuwamba, 2025 ba, duk da cewa an tattara takardun ƙarar tare da miƙa su ga kotun.
Sai dai Legit Hausa ba ta tabbatar da zargin ɓacewar fayil ɗin ko rashin takardar amsar ƙara da kanta ba, kuma kotun ba ta fitar da wata sanarwa a bainar jama’a kan batun ba.

Source: Facebook
Nafi Bala zai fara kamfen
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsagin jam’iyyar ADC, ƙarƙashin jagorancin Nafiu Bala Gombe, ya sanar da kafa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa na Ƙasa gabanin babban zaɓen 2027.
Sanarwar ta bayyana cewa kwamitin zai jagoranci tsara dabarun siyasa, daidaita ayyukan yaƙin neman zaɓe a faɗin ƙasar da kuma tattara goyon bayan 'yan Najeriya.
An naɗa Nafiu Bala Gombe a matsayin shugaban Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa, yayin da aka naɗa Farfesa Ahmed Jidda Balarabe a matsayin darakta-janar na kwamitin.
Asali: Legit.ng
