InnalilLahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Kashe Sheikh Yahaya Masussuka a Kofar Gidansa
- Waus mahara da ake zaton yan bindiga ne sun kashe babban malamin musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka a jihar Katsina
- Rahotanni sun nuna cewa maharan sun bude wa malamin wuta tare da wani almajirinsa a kofar gidansa da ke Dutsinma a daren yau Litinin
- Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar Malam Masussuka sakamakom harin da aka kai masa har gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Rahotannin da muka samu yanzu hana sun nuna cewa yan bindiga sun kashe fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka a jihar Katsina.
An ce wasu da ake zargin yan bindiga ne suka harbe malamin a kofar gidansa da ke cikin garin Dutsinma, karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina.

Source: Facebook
Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kashe Sheikh Masusuka ga tashar DW Hausa a daren yau Litinin, 26 ga watan Oktoba, 2026.
Rahotanni sun nuna cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe Sheikh Yahaya Masussuka, a gidansa da ke garin Dutsin-Ma, Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren yau Litinin a ƙofar gidan malamin, inda maharan suka buɗe masa wuta tare da wani da aka ce almajirinsa ne
Bayanai aun nuna cewa an garzaya da su zuwa Asibitin Dutsin-Ma domin samun agajin gaggawa, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsu.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu ƙarin bayani kan waɗanda suka aikata kisan ko kuma dalilin kai harin. Lamarin ya ƙara jefa al’ummar yankin cikin alhini, musamman mabiyan malamin da waɗanda suka san shi.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng
