APC Ta Koyi Hankali, Ta Ce Abin da Ya Faru a Legas Ba Zai Maimaitu a 2027 ba
- Jam’iyyar APC mai-ci ta koyi darasi da abin da ya faru da ita a zaben shugaban kasa na 2023 a jihar Legas
- Musiliu Obanikoro ya ce kwamitin yakin zaben jam’iyyar su zai kara kaimi wajen samun nasara a badi
- sanata Obanikoro yake cewa APC ta samu karin mutum miliyan guda da aka yi wa rajista wannan karo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Lagos - Jam’iyyar APC ta reshen jihar Legas ta ce ba za ta bari a sake samun irin kayen da ta sha a shekarar 2023 ba.
A zaben shugaban kasa da ya wuce, APC tana ji tana gani Peter Obi na jam’iyyar LP ya doke Bola Ahmed Tinubu a gidansa.

Source: Facebook
Shirin da APC ta ke yi a jihar Legas
Daily Trust ta rahoto Sanata Musiliu Obanikoro yana bayanin yadda jam’iyyar APC ta shirya tunkarar zaben wannan karo.

Kara karanta wannan
A lokacin da ake rokon talaka ya kara hakuri, an saya wa matasan APC motocin 'N1bn'
Daraktan yakin neman zaben PBAT-KOH, yake cewa jam’iyyar na da burin samun kusan kuri’u miliyan uku a Legas kawai.
Tsohon ministan tsaron ne yake jagorantar tallar Shugaba Bola Tinubu da ɗan takarar APC na gwamnan Legas, Kadri Hamzah.
APC ta dauki darasi da zaben Legas a 2023
Ya ce kayen da Tinubu ya sha a Legas a 2023 ya zama darasi ga jam’iyya mai mulki tun a 2015.
“Abin da ya faru a wancan lokacin (2023), ina so in gaya muku cewa ya zama farkar da mu daga barci, kuma mun farka,”
“Kun san abin da ke faruwa idan aka farkar da damisa mai tsananin yunwa? Labari ne mara daɗi. Abin da ’yan adawa suka yi ke nan. Sun farkar da damisa mai yunwa, kuma za ta yi ruri.”
- in ji Obanikoro.
Jam'iyyar APC ta samu karin magoya baya
Musiliu Obanikoro ya bayyana cewa APC ta samu kusan mambobi miliyan daya a Legas, kuma tana fatan su ba ta kuri’a.
Darektan yakin zaben ya kuma sanar da cewa Hamzat zai bayyana manufofinsa a ranar Juma’a, 30 ga Oktoba 206.
Jam’iyyar za ta gudanar da kamfen a faɗin jihar tare da tattaunawa da shugabannin addinai da sarakunan gargajiya.
APC za ta hada-kai da matasa, ’yan kasuwa da sauran al’umma domin samun goyon bayansu a zaben shekara mai zuwa.
“A karon farko a tarihin jam’iyyarmu, mun yi wa mambobi kusan miliyan ɗaya rajista. Tuni mun samar da mafita ta hanyar kara yawan mambobinmu,”
Da yake bayanin yadda jam’iyyar ta kididdige kuri’un da take sa ran samu, The Guardian ta rahoto Obanikoro ya ce:
“Ko da a ce 70% ko 80% na mambobinmu ne za su fito, kuma za su fito ɗin, wannan kaɗai zai ba mu kuri’u 800,000.

Source: Twitter
Bola Tinubu ya samu goyon bayan malamai
Ana da labari cewa a jihar Katsina, malaman Izala da na Darika sama da 1,100 suna tare da gwamnatin APC mai-ci.
Sheikh Aminu Usman wato Abu Ammar ya ce sun amince su bi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a takarar 2027.
Malaman sun fada wa Ibrahim Kabir Masari ba don abin duniya suke goyon bayan APC ba illa don cigaban Najeriya kurum.
Asali: Legit.ng
