Kwankwaso da Obi: Rigima Ta Kunno Kai bayan Kafa Kwamitin Yakin Neman Zaben NDC

Kwankwaso da Obi: Rigima Ta Kunno Kai bayan Kafa Kwamitin Yakin Neman Zaben NDC

  • Obi-Kwankwaso Movement ta zargi NDC da jinkirin shirya tsarin yaƙin neman zaɓen babban zaɓen 2027
  • Darakta-Janar na ƙungiyar, John Ughulu, ya yi ikirarin cewa kashi 90 cikin 100 na waɗanda aka naɗa a kwamitin yaƙin neman zaɓen NDC za su nemi taimakonta
  • Rikicin na ƙara tsananta ne kan yadda za a tsara tafiyar yaƙin neman zaɓen Peter Obi da mataimakinsa, Rabiu Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar Obi-Kwankwaso Movement ta soki jam’iyyar NDC kan sanar da sunayen mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓenta ta Ƙasa, inda ta nuna shakku kan shirye-shiryen jam’iyyar na tunkarar babban zaɓen 2027.

Ƙungiyar ta kuma yi ikirarin cewa tana da ingantaccen tsarin siyasa a matakin ƙasa wanda ya fi na wasu masu fafutukar neman mulki ƙarfi.

An soki NDC kan kafa kwamitin kamfe
Peter Obi tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taron NDC Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Darakta-Janar na ƙungiyar, John Ughulu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja ranar Litinin, 26 ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NDC ta kori dan takararta kan zargin tallata Atiku Abubakar

An fitar da sanarwar ne kwana guda bayan NDC ta sanar da sunayen mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓenta gabanin bikin ƙaddamar da shi a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Ƙungiyar ta zargi NDC da jinkiri

Ughulu ya ce NDC ta ɗauki lokaci mai tsawo kafin ta tsara tsarin gudanar da yaƙin neman zaɓenta, yana mai gargaɗin cewa burin siyasa kaɗai ba zai tabbatar da nasarar zaɓe ba idan babu ingantaccen tsarin wayar da kan masu zaɓe da haɗin kai a matakin ƙasa.

Ya yi ikirarin cewa ƙungiyarsa ta riga ta gudanar da shirye-shiryen da suka dace, yayin da wasu ke fara tsara nasu tsarin ne a wannan lokaci.

A cewarsa, wasu daga cikin waɗanda aka naɗa a kwamitin yaƙin neman zaɓen NDC na iya zuwa neman taimakon ƙungiyar domin samun damar amfani da tsarin da take da shi wajen tattara magoya baya.

"Abin dariya a cikin wannan jerin sunayen shi ne, kashi 90 cikin 100 na mutanen da ke cikinsa za su zo suna ƙwanƙwasa ƙofar Obi-Kwankwaso Movement suna roƙon tsarin da suka gaza ginawa da kansu!” In ji shi.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya sake kalubalantar Atiku, ya kafa kwamitin kamfen na 2027

An tambayi NDC kan shirye-shiryenta

Darakta-Janar ɗin ya kuma nuna damuwa kan lokacin da NDC ta ɗauka kafin ta sanar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa.

"Yayin da ƙasa da watanni uku suka rage kafin babban zaɓen, yanzu suke sanar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa. Me suke yi duk tsawon wannan lokacin? Ina tsarin da suke da shi? Ina dabarunsu? Ina kayan aikin da ake buƙata domin gudanar da babban zaɓen ƙasa?” In ji shi.

Saɓani kan tafiyar Obi da Kwankwaso

Sukar ta zo ne a lokacin da saɓani tsakanin NDC da Obi-Kwankwaso Movement ke ƙaruwa kan matsayin ƙungiyar da kuma yadda za ta gudanar da ayyukanta a cikin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar.

Ana danganta ƙungiyar da tafiyar siyasar Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, da mataimakinsa Rabiu Kwankwaso.

Sai dai, abin da ke ƙara fitowa fili shi ne rashin jituwa kan tsarin gudanarwa da rawar da ƙungiyar za ta taka wajen tattara magoya baya da taimakawa yaƙin neman zaɓen ’yan takarar.

Kara karanta wannan

Matsala sabuwa ta tunkaro gwamnatin Shugaba Bola Tinubu

OK Movement ta yi korafi kan kwamitin NDC
Kwankwaso tare da Peter Obi a wajen taron jam'iyyar NDC Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

NDC ta kori dan takararta

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar NDC a Jihar Borno ta kori ɗaya daga cikin ’yan takararta na Majalisar Dokokin jihar, Mohammed Bunu.

Jam'iyyar NDC ta kori dan takarar ne bisa zargin tallata ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng