Abdul Rahman Rashid
4128 articles published since 17 May 2019
4128 articles published since 17 May 2019
Wani tsohon mataimakin kwamishanan yan sanda, Hamza Idris Malikawa, ya rigamu gidan gaskiya. Marigayin ya mutu ne a jihar Kano ranar Litinin, 4 ga watan Mayu.
Gwamnatin jihar Kogi ta ce ta gano tuggun da ake kullawa na neman ta dole sai an shigo da kwayoyin cutar korona cikin jihar ta kowace irin haramtacciyar hanya.
Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya watau NCDC ta sanar da samun karin mutane 245 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Litinin.
Gwamnatin jihar Taraba ta ki amincewa da yara Almajirai 100 da gwamnatin jihar Nasarawa tayi kokarin kawo mata saboda ya sabawa yarjejeniyar kungiyar gwamnoni.
Duk da dai likafar annobar cutar korona tana ci gaba babu sassauci, gwargwado ana samun wani kaso na adadin wadanda suke samun waraka daga cutar kuma su mike.
A halin yanzu, kasashen da annobar cutar korona ta durkusar sun bazama wajen neman bashi daga cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya kamar Bankin Duniya da IMF.
Gwamnatin jihar Legas ta sallami sabbin mutane 14 da suka samu waraka daga muguwar cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus a ranar Litinin, 4 ga Mayu.
Alhaji Umar Ibn Kyari Al Amin El-Kanemi, babban dan arigayi Shehun Bama, Alhaji Kyari Ibn Umar Al Amin Ibn Ibrahim El Kanemi, ya zama sabon Shehun masarautar.
Tun bayan bullar cutar korona karo na farko a Kanon a watan Afrilu, ana ci gaba da samun yawan mace-macen mutane mai ban mamaki sabanin yadda aka saba a baya.
Abdul Rahman Rashid
Samu kari