EFCC: Cutar korona ba za ta hana yaki da rashawa ba

EFCC: Cutar korona ba za ta hana yaki da rashawa ba

Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati, ta sha alwashin ci gaba da gudanar da harkokin da aka santa a kai duk da yadda annobar korona ta dagula al'amura a kasar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, EFCC ta sha alwashin ci gaba da shari'ar da shigar a kotuna daban-daban a kan wadanda ta ke zargi da yiwa tattalin arzikin kasar nan zagon kasa.

Babu shakka alamu sun nuna cewa, takunkuman da aka shimfida a kasar na hana fita da kuma kulle da manufar dakile yaduwar annobar korona, na iya kawo cikas ga yaki da cin hanci da rashawa da Hukumar EFCC ta sanya gaba.

Sai dai duk da hakan, Hukumar ta ce tangardar da cutar korona ta kawo ba za ta hana a ci gaba da gudanar da bincike gami da tankade da rairayen da ta ke yi a kan masu yiwa tattalin arzikin kasar ta'annati ba.

A duk sa'ilin da kurar annobar korona ta lafa kuma al'amura suka cigaba da gudana kamar a baya, babu shakka Hukumar EFCC na daya daga cikin ma'aikatun gwamnatin da za su mamaye kanun labarai duba da tarin kararraki da harkokin shari'a da za su kankama a kotunan kasar nan.

Shugaban Hukumar EFCC; Ibrahim Magu

Shugaban Hukumar EFCC; Ibrahim Magu
Source: UGC

Rahotanni sun tabbatar da cewa, Hukumar ta cika hannunta makil da bincike gami da dakon kararrakin wadanda ta ke zargi da rashawa da za ta ci gaba da sauraro a kotu, yayin da tuni wasu hukuncinsu kawai ta ke jira a zartar.

Daya daga cikin wadanda EFCC ke dakon shari'arsu shi ne, Kenny Martins, babban jami'a da ake zargi ya yi ruf da ciki kan kimanin Naira biliyan 7.7 na Asusun samar da kayan bukata na hukumar 'yan sandan kasa PEF.

Sauran miyagun da ake zargi da yin sama da fadi da dukiyar gwamnati wanda hukumar EFCC ke kirdadon kurar annobar korona ta lafa domin taso keyarsu sun hadar da;

Ga jerin sunayensu da kuma mukaman da suka rike:

Doyin Okupe - Hadimin tsohon shugaban kasa Jonathan;

Babachir Lawal - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya;

Isma'ila Mustapha - Mashahuri a dandanlan sada zumunta;

Cif Fani Kayode -Tsohon ministan sufuri na jiragen sama;

Mrs. Esther Nenadi Usman - Tsohuwar karamar ministan kudi;

Sanata Gabriel Suswam - Tsohon gwamnan jihar Benuwe;

Andrew Yakubu - Tsohon shugaban kamfanin man fetur na kasa NNPC;

Sanata Adeseye Ogunleye - Tsohon Ministan ayyuka;

Malam Ibrahim Shekarau - Tsohon gwamnan jihar Kano;

Bashir Wali - Tsohon ministan harkokin waje;

Patience Jonathan - Matar tsohon shugaban kasa Jonathan;

Air Marshal Adeola Amosu - Tsohon shugaban hafsin sojin sama;

Sanata Jonah Jang - Tsohon gwamnan jihar Filato;

Sanata Saidu Kumo - Tsohon wakilin shiyyar Gombe ta Tsakiya a majalisar dattawa;

Ibrahim Shema - Tsohon gwamnan jihar Katsina;

Dr. Waripamo-Owei Dudafa - Hadimin tsohon shugaban kasa Jonathan.

Mukaddashin shugaban hukumar, Ibrahim Magu ya bayyana cewa, za su ci gaba da bin diddigin duk kararrakin da suka shigar a gaban kotu domin tabbatar da adalci da kuma sauke nauyin amanar da ta rataya a wuyansu.

A cewarsa, Hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zato da kuma kyakkyawan tsammanin da ake mata na cin nasarar yaki da rashawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel