Tabarkallah: An sallami mutane 60 daga asibiti bayan sun warke daga Coronavirus

Tabarkallah: An sallami mutane 60 daga asibiti bayan sun warke daga Coronavirus

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-olu, ya sanar da labarin sallamar masu jinyar cutar Coronavirus 60 yau Talata, 5 ga watan maris, 2020 a jiharsa kadai.

Gwamnan ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na Tuwita da yamm.

Ya ce mutane 60 da aka sallama sun hada da maza 40 da mata 20.

Kawo yanzu, jihar Legas ta sallami mutane 321 da tayi jinya a asibitocinta da cibiyoyin killacewa.

Yace, “A yau, mun sallami majinyatan COVID-19 60; maza 40 da mata 20, daga cibiyoyin killacewanmu dake Yaba, Eti-Osa da Ibeju-Lekki kuma sun koma wajen iyalansu.

“Marasa lafiyan 31 daga asibitin Mainland Infectious Disease Hospital, Yaba; 19 daga Ibeju-Lekki sannan 10 daga Eti-Osa sun samu yanci ne bayan an tabbatar da murmurewarsu kuma gwaji biyu daban-daban sun tabbatar da sun waraka.“

“Yanzu haka, adadin masu cutar COVID19 da akayi jinya kuma aka sallama a jihar Legas ya kai 321.”

KU KARANTA Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 245 sun kamu da Korona; Legas, Kano, Katsina da Jigawa ke kan gaba

Tabarkallah: An sallami mutane 60 daga asibiti bayan sun warke daga Coronavirus

Coronavirus
Source: Depositphotos

A ranar Litinin, mutane 14 da suka samu waraka daga muguwar cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus aka sallama a jihar Legas.

Ma'aikatar lafiyar jihar ta sanar da hakan ne a shafinta na Tuwita.

A bangare guda, Gwamnatin jihar Kano ta sanar da sallamar mutane uku daga cibiyar killacewanta bayan gwaji biyu daban-daban sun nuna cewa sun samu waraka daga cutar ta Korona.

Shugaban kwamitin yaki da cutar Coronavirus na jihar, Dr Tijjani Ibrahim, ya bayyana hakan yayinda hira da manema labaran kwamitin.

Kawo yanzu, jihar Kano ta zarcewa birnin tarayya Abuja a yawan masu dauke da cutar ta COVID-19. Hukumar NCDC ta tabbatar da cewa mutane 365 suka kamu a Kano.

Wannan shine karo na farko da jihar Kano za ta sallami wasu cikin masu jinyar cutar a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel