'Kebbi Taka ce': Gwamna Ya Yi Alƙawari ga Tinubu, Ya Sha Alwashi kan Zaɓe

'Kebbi Taka ce': Gwamna Ya Yi Alƙawari ga Tinubu, Ya Sha Alwashi kan Zaɓe

  • Jam’iyyar APC a Kebbi ta shirya gagarumin gangamin hadin kai na mutum miliyan daya domin nuna goyon baya ga Bola Tinubu
  • Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa dimbin jama’ar da suka halarta na nuna cewa al’ummar Kebbi suna tare da APC
  • Jami’an APC ciki har da sanatoci, ‘yan majalisar wakilai da tsoffin gwamnoni sun halarci taron, inda suka nuna kwarin gwiwar samun kuri’u masu yawa a 2027

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Birnin Kebbi, Kebbi - Birnin Kebbi ya cika da jama’a yayin da jam’iyyar APC ta shirya gagarumin gangamin hadin kai na mutum miliyan daya.

An tabbatar da cewa jam'iyyar ta yi wannan gangamin ne domin nuna goyon baya ga Bola Tinubu da Gwamna Nasir Idris.

Gwamna ya ba Tinubu tabbaci kan zaben 2027
Gwamna Nasir Idris yayin da ya ziyarci Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: @NasiridrisKG.
Source: Twitter

Gangamin ya samu halartar magoya bayan jam’iyyar daga kananan hukumomi 21, inda Gwamna Idris ya iso filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello kafin ya nufi filin taron, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Cin bashi: Fadar shugaban kasa ta yi wa Sanusi II martani kan sukar Tinubu

Alkawarin da Gwamna Idris ya yi ga Tinubu

Da yake jawabi, Gwamna Idris ya bayyana cewa Kebbi tana tare da Tinubu, yana mai danganta hakan da ayyukan ci gaba da aka aiwatar cikin shekaru uku da suka gabata.

Ya ce yawan jama’ar da suka halarta shaida ce cewa al’ummar Kebbi suna tare da jam'iyyar APC, yana mai jaddada cewa kuri’unsu za su tafi ga jam’iyyar a zaben 2027.

Sanarwar ta ce:

“Muna da dukkan dalilan da za su sa mu mara wa Shugaba Tinubu baya. Tasirin gwamnatinsa a bayyane yake, kuma al’ummarmu na iya tabbatar da irin ci gaban da aka samu cikin ‘yan shekarun da suka gabata."
Tinubu ya samu gagarumar goyon baya daga Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris yayin taro a Birnin Kebbi Hoto @NasiridrisKG.
Source: Facebook

Hadin kan da APC ke da shi a Kebbi

Gwamnan ya bayyana hadin kai da ake ciki a cikin jam’iyyar APC a jihar a matsayin alama mai ƙarfi da ke nuna ci gaba da goyon baya ga shugaban ƙasa da kuma jagorancin jam’iyyar.

“Yau rana ce ta tarihi a gare mu baki ɗaya. Ina matuƙar farin ciki da hadin kai da ake samu a cikin jam’iyyarmu da kuma tsakanin al’ummar Kebbi.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya gana da Shugaba Tinubu, an ji abin da suka tattauna

“Wannan hadin kai ya nuna karara cewa Kebbi na nan daram tare da APC da kuma jagoranmu, Shugaba Bola Tinubu."

- Nasir Idris

Sakataren shirye-shirye na kasa na jam’iyyar, Suleiman Argungu, ya nuna kwarin gwiwar cewa APC za ta samar da kuri’u sama da miliyan daya ga shugaban kasa a zaben, cewar Daily Nigerian.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai sanatoci uku na jihar, ‘yan majalisar wakilai da tsofaffin gwamnoni, ciki har da Adamu Aliero, Atiku Bagudu da Usman Nasamu Dakingari.

Gwamna Inuwa ya yi wa Tinubu alkawari

A baya, kun ji cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cikakken goyon bayansa ga shugaban kasa Tinubu a zaben 2027, yana mai cewa Gombe za ta tsaya masa tsayin daka.

Inuwa Yahaya ya ce Tinubu ya zuba jari sosai a harkar kiwo, wanda ya haifar da ci gaba, samar da aiki da inganta rayuwar al'umma musamman a Arewacin Najeriya.

Gwamnan ya jinjina wa shugaban kasa bisa amincewa da Naira biliyan 120 domin ci gaban kiwo, yana mai cewa ba a taba haka cikin shekara 47 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.