Yanzu-yanzu: An sallami mutane 14 daga asibiti bayan waraka daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 14 daga asibiti bayan waraka daga Coronavirus

Gwamnatin jihar Legas ta sallami sabbin mutane 14 da suka samu waraka daga muguwar cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus a ranar Litinin, 4 ga watan Mayu, 2020.

Ma'aikatar lafiyar jihar ta sanar da hakan ne a shafinta na Tuwita inda tace:

“An sake sallaman masu jinyar COVID-19 14; mata 6 da maza 4, duka yan Najeriya daga cibiyoyin killacewarmu dake Yaba, LUTH da Eti-Osa kuma an hadasu da iyalansu.

Marasa lafiya; 7 daga cibiyar killacewan Onikan, 2 daga Yaba, 4 daga LUTH da kuma 1 daga Eti-Osa sun samu cikakken waraka bayan gwaji biyu da akayi sun nuna haka."

"Yanzu, adadin wadanda aka yi jinya kuma aka sallama a jihar Legas sun kai 261."

"Kawo ranar 3 ga Mayu, sabbin mutane 39 sun kamu da cutar. Jimilla a Legas 1,123."

KU KARANTA: 4 a cikin 'yan Najeriya 10 su na fama da talauci - Kididdigar NBS ta nuna karuwar talauci da kaso 40

A halin yanzu adadin wadanda suka warke daga cutar korona a Najeriya sun kai 400 kamar yadda alkalumman Hukumar Dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC suka nuna.

A ranar Litinin, 4 ga watan Mayu, taskar bayanai daga shafin NCDC sun nuna cewa, an sallamo mutane 20 bayan sun warke daga dakunan jinya da wuraren killace masu cutar da ke birnin Tarayya Abuja.

A jihar Legas ne aka samu mutum 247 wadanda suka warke. Wannan shi ne adadi mafi yawa na mutanen da suka warke a jiha daya cikin dukkanin jihohin da cutar ta bulla a kasar.

Birnin tarayya Abuja ya biyo baya da adadin mutum 20 da suka murmure.

Jihar Osun ta biyo baya da mutum 22, yayin da jihohin Ogun, Edo, da kuma Akwa Ibom aka sallami mutum 10 daga kowanensu bayan samun waraka daga cutar.

Mutum 9 ne aka samu sun murmure bayan kamuwa da cutar a jihar Oyo kamar yadda alkaluman NCDC sun tabbatar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel