Sarauniyar Kasar Hausa Ta Ayyana Shiga Takarar Kujerar Sanata a Jihar Zamfara
- Hajiya Lubna Baba Gusau, fitacciyar ’yar kasuwa kuma mai taimakon al'umma, ta ayyana shiga takarar Sanatan Zamfara Ta Tsakiya a zaɓen 2027.
- Hajiya Lubna, wadda ita ce mace ta farko da ta fito takarar a ƙarƙashin jam'iyyar APC a shiyyar, ta samu taraba daga dubban magoya bayanta
- Sarauniyar Kasar Hausa ta yi alƙawarin ba da fifiko ga ci gaban mata, matasa, da kuma marasa galihu idan har ta samu nasarar lashe zaben mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Zamfara – Siyasar jihar Zamfara ta ɗauki sabon salo yayin da Hajiya Lubna Baba Gusau ta bayyana aniyarta ta neman kujerar sanata mai wakiltar shiyyar Zamfara Ta Tsakiya.
Hajiya Lubna ta yi wannan sanarwa ne a yammacin ranar Juma’a, 24 ga watan Afrilu, 2026, a gaban cincirindon magoya baya da suka fito domin yi mata maraba bayan dawowarta daga wata tafiya.

Source: Facebook
Masu goyon baya daga garuruwan Tsafe, Kotorkoshi, Damba, da Gusau sun cika tituna suna nuna godiya ga ayyukan jin ƙai da take gudanarwa, i ji rahoton The Guardian.
Manufar Hajiya Lubna ga ci gaban Zamfara
Kafin ta ƙarasa babban birnin jihar, ta tsaya a fadar Sarkin Tsafe, Alhaji Muhammad Bawa, domin neman tabaraki da addu'o'in masarautar kan wannan gagarumin takara da ta sanya a gaba.
Hajiya Lubna, wadda Sarkin Daura ya naɗa a matsayin Sarauniyar Kasar Hausa sakamakon taimakon marasa ƙarfi, ta bayyana cewa burinta na kawo ci gaba ne ya sanya ta shiga takarar.
Ta jaddada cewa wakilcin nata zai zama na daban, inda ta ce:
"Na ayyana aniyata ta shiga takarar sanata a 2027 ne domin samar da ci gaba. A matsayina na mace mai neman wakiltar Zamfara Ta Tsakiya, ina tabbatar muku da sadaukarwa ta ga kyautata mazabata da ma jihar baki daya, musamman mata, yara, matasa, da marasa galihu."

Kara karanta wannan
2027: An fara tsoron sanatan APC zai raunana aikin Tinubu bayan gana wa da Atiku Abubakar
Alkawurran Hajiya Lubna ga 'yan Zamfara
A shafinta na Facebook, Hajiya Lubna ta bayyana tafiyar tata a matsayin "Tafiyar Bege" wadda ke kunshe a ƙarƙashin ajandarta mai suna S.E.E.D for Progress.
Ta bayyana cewa wannan yunƙurin tushe ne na ’yantarwa da haɓaka mazabar Maru-Bungudu da kuma Gusau-Tsafe.
Da take jawabi ga dubban jama'ar da suka tarbe ta a Gusau, ’yar takarar ta nuna matukar farin cikinta da yadda mutane suka tsaya a cikin rana, wasu ma ba takalmi, domin nuna mata ƙauna.
"Ina yin alkawarin ba zan ba jihar tawa kunya ba, kuma mazaɓata ba za ta yi nadamar ba ni wakilci ba. Allah ya ba mu sa'a, Allah ya saka da alheri. Nagode, nagode, nagode." — Hajiya Lubna Baba Gusau.
Karanta sakonta a kasa:
Tasirin Hajiya Lubna a siyasar Zamfara
Shigar Hajiya Lubna cikin wannan takara a ƙarƙashin jam'iyyar APC ya nuna cewa mata sun fara fitowa fili domin fafatawa a manyan muƙaman siyasa a Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan
Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari
Masu sharhi na ganin cewa kasancewar ta Sarauniyar Kasar Hausa da kuma ayyukan jinkai da ta dade tana yi, za su zama babban makami a gare ta yayin da yaƙin neman zaɓen 2027 ke ƙara karatowa.
Sarauniyar Kasar Hausa ta kafa tarihi
A wani labari, mun ruwaito cewa, Sarauniyar Kasar Hausa, Lubna Mohammed Gusau, ta kafa tarihi a shekarar 2025 lokacin bikin Hawan Sallar Gani da aka gudanar a Daura, jihar Katsina.
Sarauniya Lubna ta zama mace ta farko a tarihin ƙasar Hausa da ta shiga cikin wannan gagarumin biki na al’adar malam Babaushe.
Da kwarjini da kwalliya ta sarauta, Dr. Lubna Gusau ta kayatar da dubban jama’a, inda bikin ya wuce nuna al’ada kadai, ya koma shaida ta haɗin kai, ci gaba da karfafa gwiwar malam Bahaushe.
Asali: Legit.ng
