Bayan Ta da Hankalin Trump da matarsa, an Gano Wanda Ya Kai Hari yayin Liyafa

Bayan Ta da Hankalin Trump da matarsa, an Gano Wanda Ya Kai Hari yayin Liyafa

  • An samu karin bayani game da wanda ya kai hari a Fadar White House yayin Donald Trump da matarsa ke halartar liyafa
  • Mutumin mai suna Cole Allen daga California ya kai hari da bindiga a wurin liyafar ‘yan jarida a Washington, inda aka fitar da Trump cikin gaggawa
  • Rahotanni sun ce Allen mai shekara 31 ya shiga otel ɗin Washington Hilton dauke da makamai, ya harba harsasai kusa da wurin binciken tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US — Jami'an tsaro sun gano bayanai kan mutumin da ya kai hari a Washington yayin bikin liyafa.

An gano mutumin da ya bude wuta a liyafar ‘yan jarida ta Fadar White House a daren Asabar da suna Cole Allen daga Torrance, California.

An cafke wanda ya kai wa Trump hari a White House
Matashin da ake cafke da ake zargi da kai hari da bindiga a White House. Hoto: Find Richard Holliday.
Source: Facebook

Shugaba Donald Trump ya kira shi “mahaukacin mutum” wanda ya “yi kama da mugun hali, cewar rahoton New York Post.

Kara karanta wannan

Wani mutumi ya harba bindiga a gidan gwamnatin Amurka, Trump ya kira sunan Iran

Bayanai sun fito kan mahari a Washington

Allen mai shekara 31 ya shiga otel ɗin Washington Hilton inda aka gudanar da taron, sannan ya nufi dakin taro inda Trump da baki kusan 2,500 suke.

Jami’an DSS sun gaggauta fitar da Trump daga wurin yayin da ministoci suka buya a karkashin tebura kafin a fitar da su.

Wani jami’in tsaro ya samu harbi amma rigar kariya ta hana shi rauni mai tsanani wanda ake ba shi kulawa.

Bayanan LinkedIn sun nuna Allen malami ne a C2 Education, kuma ya kammala karatu a Kwalejin Fasaha da ke California a 2017.

Trump da matarsa sun sha da kyar bayan hari a taron White House
Cole Tomas Allen da ake zargin ya kai wa su Trump hari, Donald Trump Hoto: Find Richard Holliday /Donald J Trump.
Source: Getty Images

Martanin yan sandan Washington kan lamarin

Shugaban ‘yan sandan Washington, Jeffrey Carroll, ya ce Allen na dauke da bindiga mai tsawo, karamar bindiga da kuma wukake da dama, cewar BBC.

Ya kara da cewa alamu sun nuna shi kadai ne ba tare da wata kungiyar ba.

An tuhume shi da amfani da bindiga wajen aikata laifi da kuma kai hari kan jami’in gwamnati, jami’an FBI sun kai samame gidansa a Torrance domin bincike mai zurfi.

Kara karanta wannan

Jami'ai sun kai wa Trump da matarsa dauki bayan ɗan bindiga ya kai hari taron White House

Ta ce ya ji karar harbi amma da farko ya yi tunanin wani abu ne ya fadi shiyasa bai mai da hankali ba.

Ya ce:

“Na ji kara, na dauka tire ne ya fadi ko kuma harsashi, ina fatan tire ne.”

Shugaban ya jinjina wa jami’an tsaro bisa saurin daukar mataki domin kare lafiyar al'umma.

Ya kara da cewa ba ya tunanin harin yana da nasaba da rikicin Amurka da Iran, yana mai jaddada cewa zai ci gaba da manufofinsa ba tare da tsoro ba.

An soke tattaunawar Amurka da Iran

Mun ba ku labarin cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya dakatar da tafiyar wakilansa zuwa birnin Islamabad, lamarin da ya soke zaman tattaunawa da Iran.

Trump ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne saboda yadda ake ta kwan-gaba kwan-baya kan shirya zagaye na biyu na zaman sulhu.

Bayanai sun nuna cewa Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bar birnin Islamabad bayan ganawa da jami'an Pakistan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.