Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 245 sun kamu da Korona; Legas, Kano, Katsina da Jigawa ke kan gaba

Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 245 sun kamu da Korona; Legas, Kano, Katsina da Jigawa ke kan gaba

Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya watau NCDC ta sanar da samun karin mutane 245 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Litinin, 4 ga Mayu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: An samu karin mutane dari biyu da arba'in da biyar (245) sun kamu da #COVID19. Yayinda 17 suka samu waraka, 6 sun mutu.

76-Lagos, 37-Katsina, 32-Jigawa, 23-Kano, 19-FCT, 18-Borno, 10-Edo, 9-Bauchi, 6-Adamawa, 5-Oyo, 5-Ogun, 1-Ekiti, 1-Osun, 1-Benue, 1-Niger, 1-Zamfara.

Jimilla:

Kamuwa: 2802

Sallama: 417

Mutuwa: 93

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa za ta sake kulle wasu sassan kasar nan matukar cutar coronavirus ta ci gaba da yaduwa.

Shugaban hukumar kula da hana yad war cututtuka ta NCDC, Dr Chikwe Ihekweazu, ya ce duk da hukumar na zaton za a samu masu karya doka, amma hankalinta ya tashi da yadda ta ga ana turereniya a bankuna a yau Litinin.

A yayin jawabi ga manema labarai daga kwamitin yaki da cutar , shugaban NCDC din yace: "Rahotannin farko na fadin kasar nan basu da dadin ji. Idan muka ce a kiyaye, da gaske muna nufin a kiyaye.

"Babban wurin da muka amincewa da su bude kasuwancinsu a yau sune bankuna."

"A yau za mu iya daga kafa kadan saboda ita ce rana ta farko. Amma akwai yuwuwar mu samu masu cutar da tarin yawa saboda babu wanda ya bi doka.

"Amma abu mafi muhimmanci shine yadda za mu kiyaye daga kuskurenmu a gobe. Hakan ne kadai zai sa komai ya koma daidai kafin ranar Juma'a."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel