2027: Obidients na Zargin Masoya Abba da Ƙoƙarin Yi wa Tafiyar Obi da Kwankwaso Kishiya

2027: Obidients na Zargin Masoya Abba da Ƙoƙarin Yi wa Tafiyar Obi da Kwankwaso Kishiya

  • Ƙungiyar OK Movement ta ce Peter Obi da Rabi’u Musa Kwankwaso za su tsaya wa jam'iyyar ADC takara a 2027
  • Shugaban ƙungiyar a Abuja, Jabir Ibrahim Yaro ya shaida wa Legit cewa tafiyarsu ta samu albarkar Sanata Kwankwaso da Obi
  • Ya kuma zargi wasu tsofaffin ‘yan Kwankwasiyya da ƙoƙarin kawo ruɗani a tafiyar inda suka kirkiro KO a shafukan sada zumunta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kungiyar tallata manufofin Peter Obi da Rabi’u Musa Kwankwaso, wato OK Movement, ta bayyana yakinin cewa jagororinta ne za su yi wa jam’iyyar ADC takarar shugaban ƙasa da mataimaki a zaɓen 2027.

Jabir Ibrahim Yaro, wanda aka fi sani da Malam Jabir, shugaban Obi Kwankwaso Movement a babban birnin tarayya Abuja, ne ya sanar da haka a wata hira da ya yi da Legit.

Kara karanta wannan

2027: An fara tsoron sanatan APC zai raunana aikin Tinubu bayan gana wa da Atiku Abubakar

Obi da Kwankwaso sun hade gabanin 2027
Sanata Rabi'u Musa kwankwaso tare da Peter Obi Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito a farkon mako cewa an ƙaddamar da ƙungiyar OK a babban birnin tarayya Abuja domin tallata manufofin jagororin biyu.

Da sanin manya aka haɗa OK Movement – Jabir

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa ƙungiyar OK ta ce ana iya samun masu yi mata kutse a tafiyar saboda alamun nasara da ake gani.

Da yake yi wa Legit ƙarin bayani, Malam Jabir ya ce suna sane da masu buga hotuna da ke nuna Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin mai neman takarar shugaban ƙasa.

Ya ce wannan tafiya da suka ɗauka ta tallata manufar Peter Obi a matsayin shugaban ƙasa, tare da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin mataimaki, duk da yardar manyan aka fara ta.

Ya ce:

“Idan ki ka duba mutanen da ke cikin ƙungiyar OK, mutane ne masu daraja, mutane ne waɗanda ake ji da su, mutane ne da ke kusa da duk waɗannan jagorori.”

Kara karanta wannan

Turkiyya ta yi wa ƙasashen Turai mummunan albishir kan yaƙin Rasha

“Akwai har mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiyya wanda yana cikin tafiyar."
“Ni kaina, tun kafin na zama jami’in ƙungiyar OK, ni ne daraktan Arewa maso Yamma na ƙungiyar Obidients.”

An zargi tsofaffin ‘yan Kwankwasiyya da haɗa KO

Malam Jabir ya ƙara da cewa mutanen da ke cikin Kwankwasiyya kafin ballewar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ne ke ci gaba da haɗa tafiyar KO, wato Kwankwaso Obi, maimakon Obi Kwankwaso da aka amince da shi.

Ana zargin wasu da ƙoƙarin yi wa OK kishiya
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Peter Obi Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Ya ce:

“Amma ina mai tabbatar miki da cewa wannan Obi Kwankwaso abu ne wanda dukkaninsu sun san da shi.”
“KO da mu ke gani a kafafen sada zumunta, akwai wani shafi na Kwankwasiyya Reporters wanda kowa ya sani. Bayan da gwamnan Kano ya bar NNPP, akwai mutane da yawa ‘yan Kwankwasiyya da suka bi shi, kuma a yanzu suna APC. Muna zaton su ne ke da hannu a wannan.”

Ya ƙara da cewa tun da farko APC na ƙoƙarin bata duk wani tsari da ADC ta zo da shi, don haka wannan batu bai zo musu da mamaki ba.

Kara karanta wannan

Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari

Ya ce suna da yakinin cewa Peter Obi da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne za su samu nasara a zaɓen fitar da gwani da jam’iyyar ADC za ta gudanar nan gaba.

Masoya Kwankwaso da Obi sun kafa OK

A baya, mun wallafa cewa a yayin da ake samun masu sha'awar tsayawa takara a jam'iyyar hamayya ta ADC, an ƙaddamar da Obi-Kwankwaso Movement domin tallata takarar jagororin.

Wasu jiga-jigan jam'iyya kamar Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi da Peter Obi sun nuna sha'awar neman takara a jam'iyyar, inda aka fara batun maslaha ko zaɓen fitar da gwani.

Sai dai tun kafin a kai ga batun maslaha ko zaben fitar da gwani an samar da kungiyar da ke nuna sha'warar tallata takarar Obi da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso gabanin 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng