Jaruma Mansurah Isah Ta Yi Magana kan Shirinta na Tallata Tinubu a 2027

Jaruma Mansurah Isah Ta Yi Magana kan Shirinta na Tallata Tinubu a 2027

  • Yayin da zaben 2027 ke kara karatowa, 'yan siyasa na cigaba da bayyana manufosinsu domin samun goyon bayan jama'ar kasar nan
  • Jarumar Kannywood, Mansurah Isah ta bayyana cewa za ta yi mai yiwuwa wajen tallata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027
  • Mansurah Isah ta sanar da cewa ita asalin 'yar jam'iyyar APC ce a Najeriya, inda ta ce ta shafe sama da shekara 10 tana tafiyar siyasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Jarumar fina-finai, Masurah Isah ta bayyana cewa ita 'yar jam'iyyar APC ce kuma ta shirya tallata Bola Tinubu a zaben 2027.

Jarumar ta sanar da cewa APC ta kawo cigaba sosai musamman a masana'antar Kannywood, inda aka ba jarumai da dama mukamai.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya shiga gaba, zai jagoranci 'yan adawa karfafa yaki da APC, Tinubu

Mansurah Isah da Bola Tinubu
Jaruma Mansurah Isah da hagu, Shugaba Bola Tinubu a dama. Hoto: Mansurah Isah|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Mansurah Isah ta bayyana haka ne a shirin DCL Hausa na 'siyasar zamani' kamar yadda tashar ta wallafa bidiyon a shafinta na Facebook.

Mansurah Isah za ta tallata Bola Tinubu

Mansurah Isah ta yi martani kan wani sako da aka yada a baya cewa za ta yi tsayuwar daka wajen tallata shugaban kasa Bola Tinubu.

Ta bayyana cewa ita ma a intanet ta kalli sakon ba tare da ta san daga ina ya fito ba, inda ta bukaci a rika dakar mataki kan masu yada labaran bogi.

Sai dai duk da haka, jarumar ta sanar da cewa za ta tallata shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu domin kowa yana da ra'ayinsa a siyasa.

Dangane da kalubalen da za ta fuskanta wajen masu zagi, Mansurah ta bayyana cewa dama su 'yan fim sun saba da zagi a wajen jama'a.

Yawancin 'yan fim suna jam'iyyar APC

Mansurah Isa ta bayyana cewa mafi yawan 'yan Kannywood suna goyon bayan jam'iyyar APC, yayin da wasu kadan ke goyon bayan jam'iyyun adawa.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari da EFCC ke tuhuma kan zambar N2.8bn zai fito takara a Katsina

Ta ce wasu daga cikin jaruman fim din Kannywood suna fitowa fili su yi zagi amma kuma suna halartar tarukan APC ta bayan fage.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya yana bayani a wajen taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ta kara da cewa tun da ake shugabanni a Najeriya ba a yi shugaba mai ilimi da ya jagoranci Najeriya kamar shugaba Bola Tinubu ba.

Martanin jarumi Musbahu Ahmad

Abokin tattaunawar Masurah Isah, Musbahu Ahmad, ya nuna cewa bai kamata wani mutum a Arewacin Najeriya ya tallata Bola Tinubu ba.

Jarumin ya bayyana cewa ana fama da kashe-kashe a Arewacin Najeriya kuma shugaba Tinubu ya gaza magance wannan matsalar.

Ya yi kira ga matasa da su guji sauraron mutanen da za su sauya musu ra'ayi da hanyar waka domin zaben wani shugaba a Najeriya.

Mai Sana'a ya kare Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa jarumin Kannywood, Musa Mai Sana'a ya kare salon mulkin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu.

Mai Sana'a ya bayyana haka ne bayan rade-radin da aka yi na cewa wasu matasa sun lakada masa duka saboda Tinubu a Kano.

Ya kara da cewa ba wanda ya masa duka, kuma ba gudu ba ja da baya wajen tallata shugaban kasar saboda hakan ba ridda ba ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng