Yanzu-yanzu: Wani tsohon babban jami’in dan sanda ya mutu a Kano

Yanzu-yanzu: Wani tsohon babban jami’in dan sanda ya mutu a Kano

Wani tsohon mataimakin kwamishanan yan sanda, Hamza Idris Malikawa, ya rigamu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin ya mutu ne a jihar Kano ranar Litinin, 4 ga watan Mayu, 2020, kamar yadda dan uwansa, Rilwanu, ya bayyana.

Rilwanu wanda shine jamiin yada labaran kungiyar kwallon kafar Kano Pillars yace : “An kwantar da shi a asibiti. Ya mutu ranar Litinin. Ya kasance yana fama da ciwon siga.“

KU KARANTA Yanzu-yanzu: An sallami mutane 3 masu cutar Korona a jihar Kano

Mutuwarsa ta zo kwana daya bayan mutuwar wani shahrarren mataimakin kwamishanan yan sanda a Kano.

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Atiku Nagodi, ya mutu ranar Litinin a Kano, kamar yadda SaharaReporters ta rawaito.

A cewar SaharaReporters, Nagodi ya mutu ne bayan wata gajeriyar jinya. Mutuwar Nagodi na daga cikin adadin mutanen da ke cigaba da mutuwa a Kano.

Sai dai, ya zuwa yanzu babu wasu isassun bayanai dangane da mutuwar babban jami'in dan sandan.

Kazalika, rundunar 'yan sanda ba ta fitar da jawabi ba.

Nasir Gwarzo, jagoran tawagar ma'aikatan lafiya da aka tura Kano, ya ce su na zargin cewa annobar cutar covid-19 ce sanadiyyar mutuwar mutane a jihar.

Kwararren likitan wanda ya na cikin masu yaki da annobar Coronavirus ya shaidawa manema labarai cewa sakamakon gwajin da su ka yi ya nuna COVID-19 ce ke kashe jama’a.

Gwarzo ya yi wannan jawabi a ranar Lahadi, 3 ga watan Mayu, 2020, ya ce sakamakon binciken mace - macen da ake yi a 'yan kwanakin baya bayan nan, ya tabbatar cewa akwai hannun cutar COVID-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel