Buhari ya roki IMF da Bankin Duniya su yafe bashin Najeriya

Buhari ya roki IMF da Bankin Duniya su yafe bashin Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya da su tallafawa kasashe mambobinsu wajen rage radadin da annobar cutar korona ta jefa su a ciki.

Domin neman hadin gwiwa, Buhari ya bukaci Asusun Bayar da Lamuni na Duniya da kuma Bankin Duniya, da su taimakawa kasashe mambobinsu wajen dakile mummunan tasirin da annobar cutar korona ta yi sanadi.

Daga cikin taimakon da shugaba Buhari ya nema akwai bukatar tsawaita lokacin dawo da rancen kudade, tallafin fasaha, rage jadawalin kudin fito a kan kayayyakin kiwon lafiya da kayayyakin masarufi.

Haka kuma, shugaban kasar ya bukaci a rangwantawa kasashe masu karamin karfi ta hanyar ma'amalantarsu da kwarewa a kan harkokin gudanarwa, aiwatar da manufofin kasuwancin na bai daya da kuma yafe duk basussukan da ke kansu.

A halin yanzu, kasashen da annobar cutar korona ta durkusar sun bazama wajen neman bashi daga cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya kamar Bankin Duniya da Asusun Bayar da Lamuni da sauransu.

Shugaban Najeriya; Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya; Muhammadu Buhari
Source: Twitter

Buhari ya ce hadin gwiwa a tsakanin kasashen duniya tare da tallafawa juna ita kadai ce hanyar da za ta rage tasirin da radadin annobar korona ta yi.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zage dantsen da kokarin sa ido wajen gwajin gano masu cutar da kuma tanadar wadatattun wuraren killace wadanda suka kamu da ita.

KARANTA KUMA: Jahilci ne ya ke kara tsananta cutar korona a Kano - Shehu Sani

Ya kara da cewa, akwai bukatar a kulla dabaru a tsakanin kasa-da-kasa domin shawo kan cutar korona, wanda a cewarsa, ta haifar da mummunar illa ga rayuwar al'umma, abubuwan more rayuwa da tattalin arzikin duniya.

Ya ke cewa, "makonnin biyu da suka gabata a yankin mu na Yammacin Afirka, mun gudanar da taro domin shimfida matakan dakile wannan muguwar cuta da ta zamto alakakai a fadin duniya."

Ana iya tuna cewa a yayin taron ne shugabannin kungiyar kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) suka nada shugaban Najeriya, a matsayin gwarzon da zai jagoranci yaki da annobar cutar covid-19 a yankin.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wani sako da ya wallafa kan shafinsa na Twitter a ranar 23 ga watan Afrilun 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel