Jahilci ne ya ke kara tsananta cutar korona a Kano - Shehu Sani

Jahilci ne ya ke kara tsananta cutar korona a Kano - Shehu Sani

Tsohon wakilin shiyyar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Shehu Sani, ya fito kwansa da kwarkwata wajen fayyace fahimtarsa kan dalilin da ya sanya cutar korona ta yi kamari a jihar Kano.

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, Sanata Shehu ya ce tsantsar shiga da ka ko kuma duhun jahilci shi ne musabbabin da ya ke kara ta'azzara illar annobar korona a jihar Kano da ke Arewacin kasar nan.

Tun bayan bullar cutar korona karo na farko a Kanon a watan Afrilu, ana ci gaba da samun yawan mace-macen mutane mai ban mamaki sabanin yadda aka saba a baya a fadin jihar.

An samu mafi yawan adadin sabbin mutane da cutar korona ta harba a jihar a ranakun Alhamis da Juma'a da suka gabata, inda a halin yanzu adadin masu cutar a jihar ya kai 311.

A jawaban da tsohon Sanatan ya yi a ranar Asabar, ya zargi 'yan siyasa da kuma shugabannin addinai na jihar da taka rawar gani wajen rura wutar annobar da ake fama da ita ta hanyar sabawa dokokin mahukuntan lafiya.

Ya ke cewa: "Halin da ake ciki a Kano wani mummunan bala'i ne wanda za'a iya magance shi."

"A yanayi makamancin wannan da ake bukatar gaggawa a bangaren kiwon lafiya, tarihi ya nuna yadda shugabannin addinai a Kano suke yada munanan tatsuniyoyi masu hatsari, camfe-camfe masu ban tsoro da kuma labarun almara,” in ji tsohon Sanatan.

Sanata Shehu Sani
Sanata Shehu Sani
Asali: UGC

"Sannu a hankali shugabannin siyasa a Kano suna matukar taka rawar gani wajen jefa mutane cikin duhun jahilci da kuma shiga da ka da malaman addini ke yi wa ilimin kimiya, wanda hakan yana sanya dimbin jama'a a hanyar cutarwa."

"Daga cutar shan inna zuwa ta korona, Arewacin Najeriya musamman jihar Kano a tarihi, ta zama mabubbuga kuma cibiyar hatsabiban cututtuka masu yaduwa sakamakon rashin yiwa addini kyakkyawar fahimta, da hakan ya janyo ake watsi da shawarwarin mahukuntan lafiya."

KARANTA KUMA: Coronavirus: Masu bincike na jami'ar FUTA sun bayar da shawara a kan shan shayin zobo da citta domin bunkasa garkuwar jiki

Sanata Shehu ya ce mummunar fahimta da mafi akasarin mutane a Arewa ke yiwa addini, ya sanya ake 'tarar aradu da ka' wajen kin gaskiyar da kwararru a fannin kiwon lafiya suka fadi.

"Tsabar rashin ilimi ko kuma tsunduma da aka yi cikin duhun jahilci, ya kara harzuka tsananin da annobar cutar korona ta yi a jihar Kano."

"Hanya mafi inganci da ya kamata a bi domin sauya wannan mummunan tunani daga kan al'ummar Kano ko kuma mafi rinjayen kaso na Arewa, shi ne wayar da kan malaman addini a kan kaucewa tunanin da suke yi na ganin ana kulla tuggun rage adadin musulmai."

Ya kuma ce almajiran da aka tursasawa komawa kauyukansu a yunkurin dakile yaduwar cutar korona. na iya dawowa a matsayin 'yan tawaye ko kuma 'yan ta'adda.

"Manya da kuma 'yan siyasa na Arewa na ci da addini a matsayin hanyar samun damar hawa kujerun mulki ko kuma dawwama a kansu, wanda ci gaba da yin hakan illa ne mai haifar da koma bayan tattalin arziki da dakushewar ci gaba a yankin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel