Asiri Ya Tonu: An Kama Mai Taimakawa Yan Bindiga Su Samu Kudi a Sakkwato, Ya Fara Bayani
- 'Yan sanda sun kama yan leken asirin kungiyar Lakurawa da masu taimaka wa yan ta'addan wajen samun kudi a jihar Sakkwato
- Kwamishinan yan sandan Sakkwato, Hayatu Hassan Shaffa ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a jihar
- Ya ce jami'an tsaro sun samu nasarar fatattakar yan bindiga lokacin da suka kai hari kauyukan karamar hukumar Sabon Birni
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Sokoto, Nigeria - Rundunar ‘yan sandan Sokoto ta sanar da cafke wasu da ake zargi da ba ‘yan bindiga bayanai da kuma taimaka masu wajen samun kudade.
Kwamishinan ‘yan sanda na Sokoto, Hayatu Hassan Shaffa, ya ce a ranar 17 ga Afrilu, 2026, jami’an sashen yaki da garkuwa da mutane sun kama wani Aminu Mai Roba daga kauyen Maikulki da ke karamar hukumar Binji.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta rahoto cewa da yake hira da manema labarai, ya ce an tare wanda ake zargin ne a kan hanyar Ruwa-Wuri zuwa Tangaza dauke da shanu guda hudu.
An samu bayanai daga bakin mutumin
A cewar CP Hayatu, bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya amsa cewa ya karbi shanun ne daga kungiyar ‘yan ta’adda ta Lakurawa a kauyen Wariya da ke Tangaza.
“Ya bayyana cewa aikinsa shi ne sayar da shanun sannan ya mayar da kudin ga kungiyar ‘yan ta’addan. Mun fara hada hujjoji yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.” in ji shi.
Kwamishinan 'yan sandan ya ce wannan na daga cikin kokarin rundunar wajen tabbatar da gaskiya da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin ‘yan sanda da al’umma
Ya jaddada cewa rundunar na ci gaba da kokarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da dakile aikata laifuka, kamar yadda Daily Post ta kawo.
Jami'an tsaro sun fatattaki yan bindiga
Ya kuma bayyana cewa a ranar 8 ga Afrilu, da misalin karfe 4:20 na safe, ‘yan sanda sun samu kiran gaggawa kan harin da ‘yan bindiga suka kai kauyukan Kwarengamba da Gayya da Kwari a karamar hukumar Sabon Birni
A cewarsa, jami’an ‘yan sanda tare da sojoji, ‘yan sa-kai da masu tsaron al’umma sun kai dauki cikin gaggawa.

Source: Original
Ya ce hadakar jami’an tsaron ta fafata da ‘yan bindigar inda aka fatattake su bayan musayar wuta mai tsanani.
“Maharan sun tsere da raunukan harbi zuwa cikin daji, sannan suka bar buhu dauke da harsasai 167,” in ji shi.
Kwamishinan ya yaba da kokarin jami’an tsaro, yana mai cewa nasarorin da aka samu na nuna kwarewa da jarumtaka, tare da karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro daban-daban da al’umma baki daya.
Mutane sun fara barin gidajensu a Sokoto
A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga sun addabi mutanen karamar hukumar Wurno ta jihar Sokoto da hare-haren rashin tausayi, wanda ke jawo asarar rayuka.

Kara karanta wannan
Kotu ta yanke hukunci a shari'ar Sanata Natasha da Yahaya Bello, ta umarci biyan N1bn
Bisa haka ne mazauna karamar hukumar suka fara tattara kayansu suna barin gidajensu domin guje wa hare-haren 'yan bindiga.
Shugaban ƙaramar hukumar Wurno, Alhaji Abba Isa Sadiq Achida, ya bayyana hakan yayin da yake kokawa kan matsalar rashin tsaro.
Asali: Legit.ng

