Abubuwa 11 da mutum zai yi idan ya yi cudanya da mai cutar korona

Abubuwa 11 da mutum zai yi idan ya yi cudanya da mai cutar korona

Yayin da duniya ke ci gaba da gwagwarmaya da hatsabiyayar cutar nan mai sarkewar numfashi ta korona, akwai bukatar 'yan Najeriya su samu cikakkiyar sanarwa game da matakan kare kai daga cutar.

Akwai shawarwari da matakai da dama da ya kamata mutum ya dauka a duk lokacin da ya yi cudanya da wanda kwararrun lafiya suka tabbatar ya kamu da cutar korona.

Da wannan matakai da kuma shawarwari za su iya sanya ido a kan lafiyarsu kuma za su taimaka musu wajen kaucewa yada cutar ga masu lafiya.

Ta yadda za ka gane kana da hatsarin kamuwa da cutar shi ne idan ka yi cudanya da marar lafiyar da kwararrun lafiya suka tabbatar cutar ta harbe shi.

Yadda ake amfani da takunkumin rufe fuska
Yadda ake amfani da takunkumin rufe fuska
Asali: UGC

Hanyoyin samun cudanya da wanda cutar korona ta harba:

1. Zama a gida daya da marar lafiya mai dauke da kwayoyin cutar korona.

2. Yin jinyar mara lafiya mai dauke da kwayoyin cutar korona.

3. Kasancewa a tsakanin kafa shida da wanda cutar ta harba na tsawon minti goma.

4. Yin mu'amala kai tsaye da kazantar da ta fito daga jikin mai cutar korona, kamar gumi, fitsari, yawu, da sauransu; ta hanyar tari, sumbata ko amfani da kaya daya.

Idan kowane daya daga cikin abubuwan da ke sama suka faru da kai, to dole ka dauki wadannan mataki kamar haka:

1. Killace kai idan alamomin cutar sun fara bayyana a kan ka.

2. Ka kasance a killace kanka ko da ka tunanin baka kamu da kwayoyin cutar ba, amma kananan alamominta sun fara bayyana.

KARANTA KUMA: Covid-19: Jihar Kano tana karkashin kulawa ta musamman - Gwamnatin Tarayya

3. Ko da alamomin cutar basu bayyana ba amma kayi cudanya da mai ita, to ka killace kan ka har na tsawon kwanaki 14.

4. Ga wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, su ware kansu na tsawon kwanaki 14 koda alamominta sun bace a matsayin matakan kariya.

5. Ka sanya ido a kan lafiyarka musamman lura da zazzabi, tari, da sarkewar numfashi tun daga ranar karshe bayan ka shafe kwanaki 14 a killace.

6. Ka kauracewa fita aiki ko zuwa makaranta.

7. Ka kauracewa shiga taron jama'a har na tsawon kwanaki 14.

8. Idan kana tunanin ka kamu da cutar, ka hanzarta kiran lambar wayar gaggawa da hukomin lafiya na gwamnati suka yi tanadi domin a kawo maka agaji.

9. Duk wata cibiyar lafiya da ka ziyarta ka tabbata kana sanye da takunkumin rufe hanci da baki.

10. Idan akwai dama, ka bayar da tazara ta tsawon mita daya tsakanin ka da sauran mutane.

11. Kada ka rika amfani da tafukan hannayenka wajen tabe-taben wurare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel