Yanzu-yanzu: An nada sabon Shehun Bama

Yanzu-yanzu: An nada sabon Shehun Bama

Alhaji Umar Ibn Kyari Al Amin El-Kanemi, babban dan marigayi Shehun Bama, Alhaji Kyari Ibn Umar Al Amin Ibn Ibrahim El Kanemi, ya zama sabon Shehun masarautar Bama.

Tawagar gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Jidda Shuwa, suka gabatar da wasikar ga sabon sarkin masarautar a ranar Litinin, 4 ga watan mayu, 2020.

Sauran mambobin tawagar sun hada da kwamishanan harkokin kananan hukumomi da masarautun gargajiya da Diraktan lamuran masarautu.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nada shi ne da sharadin cewa zai zauna a garin Bama ba ya rika mulkan al'ummarsa daga Maiduguri ba.

Yanzu-yanzu: An nada sabon Shehun Bama
Yanzu-yanzu: An nada sabon Shehun Bama
Asali: Facebook

KU KARNATA: An sallami mutane 14 daga asibiti bayan waraka daga Coronavirus

Sakataren gwamnatin jihar yace: "Mai girma (gwamna) ya umurceni da fada maka cewa ka zauna a Bama saboda ya nunawa jama'arka kana tare da su."

"Matsayinka na shugaba na da muhimmanci ga gudanar lamuran jama'a."

"Gwamnan jihar Borno ya nada ka ne saboda gaskiyarka da tarihin yiwa mutanen karamar hukumar Bama aiki."

"Ya kai mai martaba, wannan matsayi da gwamnan Borno ya nadaka, ana kyautata zaton za kayi adalci, daidaito da kyautatawa ga jama'an Bama."

Sakataren gwamnatin ya karkare da cewa an nada sabon Shehun ne bisa ga shawarar masu nada sarki na masarautar Bama.

Gabanin nadasa, Shehu Umar, ya kasance dan kasuwa.

Yau ta cika mako daya da tsohon Shehun Baman ya rasu.

Ya mutu ne bayan gajeruwar rashin lafiyan da yayi a asibitin koyarwan jamiar Maiduguri

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon Shehun ya rasu ne sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus da ta addabi duniya shekarar nan.

Hakazalika hakan aka bayyana game da rasuwar Jarman Kano da ya rasu, tare da Sarkin Kaura Namoda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng