Jerin kasashe da cutar korona ta fi yiwa illa a nahiyyar Afirka - WHO

Jerin kasashe da cutar korona ta fi yiwa illa a nahiyyar Afirka - WHO

- Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce an samu akalla mutane 46,547 da suka kamu da cutar coronavirus a nahiyyar Afirka

- Hukumar ta ce an samu mutane 15,000 da suka warke daga cutar yayin da ta hallaka mutum 1, 835 a nahiyyar

- Alkaluman Hukumar sun nuna Afirka ta Kudu ita ce kasar da cutar ta fi harbi da mutum 7,220, sai kuma kasar Libya a mataki na kasa da mutum 63.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce fiye da mutane 46,000 sun kamu da cutar coronavirus a kasashen nahiyar Afirka.

Duka dai mutum 1,835 ne cutar ta yi sanadiyar mutuwarsu kamar yadda hukumar lafiyar ta bayyana.

Haka kuma ta ce an samu fiye da mutane 15,000 da suka warke bayan kamuwa da cutar a kasashen na Afirka.

A wata sabuwar wallafar alkalumma da hukumar ta fitar a ranar Talata, 5 ga watan Mayun 2020, ta nuna jerin kasashen da cutar ta fi harbi a nahiyyar Afirka.

Yayin sabunta jeranton, alkaluman WHO sun nuna cewa akwai mutane 2,802 da cutar ta harba a Najeriya, wanda hakan ya yi daidai alkaluman hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC.

A sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.45 na daren ranar Litinin, 4 ga watan Mayu, adadin wadanda cutar coronavirus ta harba a kasar ya kai 2,802.

Alkalumman WHO sun tabbatar da cewa an samu mutane 7,220 da annobar ta harba a Afirka ta Kudu, 4,648 a Algeria, 2,719 a Ghana yayin da 2,077 suka harbu a kasar Kamaru.

Libiya ce kasar da har yanzu cutar korona ba ta yi wani tasirin gaske ba inda aka samu mutum 63 kacal da suka kamu.

Dubi alkalumman da WHO ta fitar:

Jerin kasashe da cutar korona ta fi yiwa illa a nahiyyar Afirka - WHO

Jerin kasashe da cutar korona ta fi yiwa illa a nahiyyar Afirka - WHO
Source: Facebook

KARANTA KUMA: Abubuwa 11 da mutum zai yi idan ya yi cudanya da mai cutar korona

A yunkurin dakile yaduwar cutar, mun ji cewa an sanya dokar tilasta amfani da takunkumin rufe da fuska a kasar Ghana.

Ministan lafiya na kasar, Kwaku Agyeman Manu, ya umurci dukkanin al'ummar kasar da su kiyaye wannan doka da aka shimfida da manufar dakile yaduwar cutar.

A cewarsa, "bari kuji in fada muku, duk mai son ya kamu da wannan cuta kuma yana son ya mutu yanzu, mu bamu shirya mutuwa ba yanzu, saboda haka dole ne mu hada kai domin mu gudu tare kuma tsira tare."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel