An sallami mutane 400 da suka warke daga cutar korona a Najeriya - NCDC

An sallami mutane 400 da suka warke daga cutar korona a Najeriya - NCDC

Duk da dai likafar annobar cutar korona tana ci gaba babu sassauci, gwargwado ana samun wani kaso na adadin wadanda suke samun waraka daga cutar kuma su mike wasai.

A halin yanzu adadin wadanda suka warke daga cutar korona a Najeriya sun kai 400 kamar yadda alkalumman Hukumar Dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC suka nuna.

A ranar Litinin, 4 ga watan Mayu, taskar bayanai daga shafin NCDC sun nuna cewa, an sallamo mutane 20 bayan sun warke daga dakunan jinya da wuraren killace masu cutar da ke birnin Tarayya Abuja.

A jihar Legas ne aka samu mutum 247 wadanda suka warke. Wannan shi ne adadi mafi yawa na mutanen da suka warke a jiha daya cikin dukkanin jihohin da cutar ta bulla a kasar.

Birnin tarayya Abuja ya biyo baya da adadin mutum 20 da suka murmure.

Jihar Osun ta biyo baya da mutum 22, yayin da jihohin Ogun, Edo, da kuma Akwa Ibom aka sallami mutum 10 daga kowanensu bayan samun waraka daga cutar.

Mutum 9 ne aka samu sun murmure bayan kamuwa da cutar a jihar Oyo kamar yadda alkaluman NCDC sun tabbatar.

A Kaduna kuma an sallami mutum 8 ciki har da gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufa'i yayin da an sallami mutum 7 bayan sun samu waraka daga cutar a jihar Kano.

Alkaluman NCDC sun nuna cewa, an sallami mutane shida daga wuraren killacewa bayan sun warke a kowane daya daga jihohin Bauchi, Katsina da kuma Kwara.

KARANTA KUMA: Buhari ya roki IMF da Bankin Duniya su yafe bashin Najeriya

A jihar Delta kuma an samu mutane 4 da suka murmure, sai kuma jihar Ondo inda mutane 3 suka mike wasai abin su.

An sallami mutane biyu daga kowane daya daga cikin jihohin Rivers, Ekiti, da Enugu. Sai kuma jihohin Anambra, Abia, Neja da kuma Sokoto inda mutum daya ya wartsake daga kowanensu.

Kididdigar alkaluman ta nuna cewa, babu ko mutum daya da aka sallama a jihohi 14 da cutar ta bulla da suka hadar da; Gombe, Borno, Yobe, Kebbi, Taraba, Adamawa, Bayelsa, Jigawa, Ebonyi, Filato, Imo, Nasarwa, Zamfara da kuma Benuwe.

A halin yanzu dai, mutane 2,558 cutar korona ta harba a duk fadin Najeriya yayin da tuni mutane 87 suka riga mu gidan gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel