"Ku Daina Kira na Bahaushe," Babban Malamin Addini Ya Gargadi 'Yan Najeriya
- Babban malamin darikar Katolika na Sakkwato, Bishop Matthew Kukah, ya bukaci ‘yan Najeriya da su daina yi masa lakabi da Bahaushe
- Bishop Kukah ya bayyana cewa shi dan asalin kabilar Ikulu ne daga karamar hukumar Zangon Kataf da ke jihar Kaduna, ba Bahaushe ba
- Ya bayyana hakan ne a yayin taron yaye dalibai na jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da ke jihar Anambra, inda aka ba shi mukami
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
AWKA, Najeriya – Fitaccen malamin addinin nan kuma sabon shugaban jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu (COOU), Bishop Matthew Kukah, ya gargadi 'yan Najeriya kan kiransa 'Bahaushe.'
Bishop Kukah, wanda shi ne babban shugaban katolita na jihar Sokoto, ya ce ba shi da wata alaka da Hausawa, don haka bai kamata a rika kiransa da Bahaushe ba.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: An kama mai taimaka wa yan bindiga su samu kudi a Sakkwato, ya fara bayani

Source: Facebook
"A daina kira na Bahaushe" - Bishop Kuka
Babban malamin addinin Kiristan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wurin taron yaye dalibai karo na 16 na jami’ar COOU a ranar Asabar, in ji rahoton Punch.
Bishop Kukah ya jaddada cewa ko da yake shi dan Najeriya ne na gari, bai kamata a rika kiransa da Bahaushe ba saboda bambancin asalinsa.
Bishop Kukah ya fayyace asalinsa kamar haka:
"Ni dan Najeriya ne na gari daga Anchuna, Masarautar Ikulu da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna, amma ni ba Bahaushe ba ne. Ya kamata 'yan Najeriya su daina kirana da ɗan Hausa."
Rantsar da sabon jagoran jami’a
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ne ya rantsar da Kukah a matsayin sabon shugaban hukumar gudanarwar jami’ar.
Kukah ya yaba wa gwamnatin jihar kan yadda take zuba jari a fannin ilimi, inda ya bayyana cewa kididdiga ta nuna Anambra na daya daga cikin jihohin da suka fi kokari a fannin ilimi a Najeriya.
Ya kuma yi alkawarin cewa karkashin jagorancinsa, jami'ar za ta zarce manufofin da aka sa gaba.
Gwamna Soludo ya nuna gamsuwarsa da nada Kukah, inda ya bayyana cewa kwarewarsa da jagorancinsa na kwarai za su kara daukaka darajar jami'ar.
Gwamnan ya bukaci jami'ar da ta ci gaba da samar da dalibai masu magance matsaloli maimakon wadanda kawai ke kirga matsalolin.

Source: Facebook
Gwamna ya karrama gwarazan dalibai
A yayin taron, Gwamna Soludo ya sanar da kyaututtuka ga daliban da suka nuna bajinta:
- Somtochukwu Augustus Ume: Dalibin da ya fi kowa hazaka daga sashin tattalin arziki tare da maki 4.85, ya samu kyautar naira miliyan 4.
- Dalibai masu daraja ta 1: Gwamnan ya ba wa dalibai 37 da suka kammala da daraja ta daya (First Class) gurbin karatu kyauta har zuwa matakin karshe a kowace jami'ar gwamnati da suka zaba.
Gwamnan ya bukaci daliban da suka kammala da su kasance masu hali na kwarai ga iyayensu, jami'ar, jihar Anambra, da ma Najeriya baki daya.
Kukah ya yi magana kan kisan kiristoci
A wani labari, mun ruwaito cewa, Bishop Matthew Kukah ya ce maganganun da ake yadawa kan cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya ba su da tushe.
Kukah, shugaban darikar Katolika na Sokoto kuma jagoran Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa, ya karyata ikirarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.
Ya ce wadannan jita-jita sun fi kama da siyasa da rashin tantance bayanai fiye da gaskiyar abin da ke faruwa a kasar nan.
Asali: Legit.ng

