Covid-19: Jihar Kano tana karkashin kulawa ta musamman - Gwamnatin Tarayya

Covid-19: Jihar Kano tana karkashin kulawa ta musamman - Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, a halin yanzu ta mayar da hankali a kan jihar Kano saboda matsalolin da suka yi wa jihar dabaibayi sanadiiyar annobar korona.

Jihar Kano tana karkashin kulawa da sa ido na musamman a sanadiyar yadda babu wani sassauci likafar annobar korona ta ke ci gaba tamkar wutar daji a jihar a cewar gwamnatin tarayya.

Duk da tana lura da halin da sauran jihohin kasar suke ciki, a yanzu haka gwamnatin ta karkatar da duk wani yunkurinta domin dakile yaduwar cutar a Kano ta hanyar fadada gwaji da kula da masu cutar a jihar.

Darakta janar na Hukumar NCDC mai kula da yaduwar cututtuka a kasar, Dr Chikwe Ihekweazu, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin birnin Abuja a ranar Litinin yayin ganawa da kwamitin kar ta kwana da fadar shugaban kasa ta kafa a kan cutar korona.

A cewarsa, "wannan ba shi ne yake nuna jihar Legas ba ta da muhimmanci a wurin mu, hasali ma ta fi duk jihohin Najeriya yawan masu cutar korona da kaso 50%.

"Saboda haka za mu ci gaba da mayar da hankali a kan jihohin biyu duba da yadda suke bukatar kulawa ta musamman."

Shugaban NCDC; Dr Chikwe Ihekweazu
Shugaban NCDC; Dr Chikwe Ihekweazu
Asali: UGC

"Sai dai duba da yadda lamarin jihar Kano ya wuce gona da iri a yanzu, muka ga ya kamata mu karkatar da akalar mu ta kulawa zuwa jihar tun kafin ya fi karfin mu."

Haka kuma mun ji cewa, Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya da ministan lafiya, Osagie Ehanire, sun bayyana a gaban majalisar wakilai ta tarayya don yin bayani a kan yawan mace-macen da ake samu a jihar Kano.

KARANTA KUMA: EFCC: Cutar korona ba za ta hana yaki da rashawa ba

Baya ga manyan jami'an gwamnatin biyu, sun kuma samu rakiyar Dr. Ihekweazu yayin da majalisar ta karbi bakuncinsu a yau Talata, 5 ga watan Mayu.

Kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa, manyan jami'an gwamnatin za kuma su yi wa majalisar bayani ne kan kokarin da suke yi wajen shawo kan annobar korona a kasar baki daya.

A halin yanzu dai, jihar Kano na da masu jinya 365 daga cikin 2,802 da ke fama da cutar korona a kasar kamar yadda alkalumman NCDC suka tabbatar.

Daga bisani kuma gwamnatin Kano ta sanar da sallamar mutane uku daga cibiyar killace masu fama da cutar korona bayan sakamakon gwaji ya nuna cewa sun warke kuma ba sa dauke da kwayoyin cutar.

Shugaban kwamitin yaki da cutar a jihar, Dr Tijjani Ibrahim, shi ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel