Ku rike kayanku - Jihar Taraba ta ki amsan Almajirai 100 da ta Nasarawa kawo mata

Ku rike kayanku - Jihar Taraba ta ki amsan Almajirai 100 da ta Nasarawa kawo mata

Gwamnatin jihar Taraba ta ki amincewa da yara Almajirai 100 da gwamnatin jihar Nasarawa tayi kokarin kawo mata saboda ya sabawa yarjejeniyar da kungiyar gwamnoni suka yi.

Shugaban kwamitin yaki da cutar Korona na jihar Taraba, Dr Innocent Vakai, ya bayyana hakan ranar Litinin a hirar da yayi da manema labarai a Jalingo, babbar birnin jihar.

Gwamnonin Najeriya sun yi yarjejeniyar cewa wajibi ne a gudanar da gwaji kan dukkan Almajiran da akayi niyyar mayarwa jiharsu ta asali.

Hakazalika wajibi ne jami'an gwamnatin jihar su raka almajiran tare da sakamakon gwajin COVID-19 da aka gudanar musu.

Dr Innocent Vakai, wanda shine kwamishanan lafiyan jihar ya ce sai an bi ka'ida kafin su karbi almajiran daga hannun jihar Nasarawa.

Vakai ya kara da cewa Talatu Idris, mai cutar Coronavirus da ta gudu daga inda aka killaceta ta shiga hannu.

Ya bayyana cewa an fara zakulo wadanda suka yi ma'amala da masu cutar a jihar don hana yaduwarta.

KU KARANTA: 4 a cikin 'yan Najeriya 10 su na fama da talauci - Kididdigar NBS ta nuna karuwar talauci da kaso 40

A halin yanzu, jihar Taraba na da mutum 8 da ke dauke da cutar coronavirus kuma ta wajabta saka takunkumin fuska na kwanaki biyun da take barin walwalar jama'a a jihar.

A gefe guda, gwamnatin Katsina ta bayar da umarnin sake rufe wasu manyan kasuwanni uku da ke ci sati - sati a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Lahadi, 03 ga watan Mayu.

Kasuwanni da wannan umarni ya shafa sune; Garkin Daura, Dusti, da Kayawa.

An rufe kasuwannin ne bayan gwamnati da ma su ruwa da tsaki sun nuna damuwarsu a kan hauhawar mutanen da ke kamuwa da cutar covid-19 a jihar Katsina.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel