Yanzu-yanzu: An sallami mutane 3 masu cutar Korona a jihar Kano

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 3 masu cutar Korona a jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da sallamar mutane uku daga cibiyar killacewanta bayan gwaji biyu daban-daban sun nuna cewa sun samu waraka daga cutar ta Korona.

Shugaban kwamitin yaki da cutar Coronavirus na jihar, Dr Tijjani Ibrahim, ya bayyana hakan yayinda hira da manema labaran kwamitin.

Kawo yanzu, jihar Kano ta zarcewa birnin tarayya Abuja a yawan masu dauke da cutar ta COVID-19. Hukumar NCDC ta tabbatar da cewa mutane 365 suka kamu a Kano.

Wannan shine karo na farko da jihar Kano za ta sallami wasu cikin masu jinyar cutar a jihar.

KU KARANTA Tabarkallah: An sallami mutane 60 daga asibiti bayan sun warke daga Coronavirus

A wani labarin daban, Sama da likitoci 30 ne a asibitocin kudi da na gwamnati a jihar Kano suka kamu da cutar korona, kamar yadda kungiyar likitoci ta kasa (NMA) ta bayyana.

Shugaban NMA na reshen jihar Kano, Dr Sanusi Mohammed Bala ya tabbatar da cewa daya daga cikin likitocin da suka kamu da cutar a jihar ya riga mu gidan gaskiya.

Ya bayyana cewa, da yawa daga cikin wadanda suka kamu da cutar sun sameta ne ta hanyar duba marasa lafiya wadanda suka zo asibitin ba tare da sun san suna dauke da cutar ba.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, goma daga cikin likitocin da suka harbu da cutar duk ma'aikata ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Shugaban likitoci masu neman kwarewa na asibiti Malam Aminu Kano, Dr Abubakar Nagoma Usman ya dora laifin halin da suke ciki da rashin kayan kariya.

Ya ce gangancin marasa lafiyan ta yadda suke boye bayanai ga likitocin ya taka rawar gani wurin yada muguwar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel