Yadda Moroko da Ƙasashen Afirka 9 Suka Taka Leda a Gasar Kofin Duniya Ta 2026
Amurka - Bayan da Morocco ta zama ƙasa ta ƙarshe daga cikin ƙasashen Afirka 10 da suka yi bankwana da gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026, lokaci ya yi da za a yi nazari kan yadda nahiyar ta taka rawar gani a gasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da 10 a aikin jarida.
Gaba ɗaya, kasashen nahiyar Afirka sun nuna ƙwazo a gasar, amma dai babu wata ƙasa da ta iya maimaita bajintar da Moroko ta yi a gasar 2022 lokacin da ta kai wasan kusa da na ƙarshe.

Source: Getty Images
Rawar kasashen Afrika a Kofin Duniya
Ga yadda kowacce ƙasa ta taka rawa a gasar kamar yadda rahoton Super Sport ya nuna:
1. Algeria
Matsayi: Zagayen 'yan 32

Source: Getty Images
An shiga gasar da kyakkyawan fata kan Algeria saboda ƙwarewar kocinta Vladimir Petković da kuma ingancin 'yan wasan da take da su. Da dama sun yi hasashen cewa ƙasar za ta iya yin nisa a gasar.
Sai dai duk da samun tikitin tsallakewa daga rukuni a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun ƙasashen da suka zo na uku, Algeria ba ta taɓa nuna cikakken ƙarfinta ba a duk tsawon gasar.
Ta fara da rashin nasara a hannun Argentina, kafin ta samu nasara a kan Jordan. Daga nan ta buga wasa mai kayatarwa da Austria wanda ya ƙare da ci 3-3, ɗaya daga cikin wasannin da suka fi ɗaukar hankali a gasar.
A zagayen 'yan 32 kuwa, Algeria ta kara da Switzerland, tsohuwar ƙungiyar kocinta Petković, inda ta sha kashi cikin sauƙi tare da yin bankwana da gasar, kamar yadda Reuters ta ruwaito.
2. Cape Verde
Matsayi: Zagayen 'yan 32

Source: Getty Images
Kafin fara gasar, mutane da dama sun yi hasashen cewa Cape Verde ba za ta iya taka rawar gani ba. Amma ƙasar ta sauya wannan ra'ayi ta hanyar nuna ƙwazo, jajircewa da kuma buga ƙwallo mai armashi.
Ta fara da kunnen doki da Spain, inda mai tsaron raga mai shekara 40, Vozinha, ya yi fice matuƙa. Daga nan kuma ta sake yin kunnen doki 2-2 da Uruguay, sakamakon da ya girgiza masu bibiyar gasar.
Rahoton BBC ya nuna cewa Canjaras da ta yi da Saudiyya ya ba ta maki uku da suka isa ta tsallake rukuni a matsayi na biyu.
A zagayen 'yan 32 ta fafata da Argentina, inda ta kai wasan har zuwa ƙarin lokaci kafin ta sha kashi da ci 3-2. Duk da ficewarta, Cape Verde ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da aka fi yabawa a gasar saboda irin bajintar da ta nuna.
3. DR Congo
Matsayi: Zagayen 'yan 32

Source: Getty Images
Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo) ta shiga gasar ne bayan fuskantar matsaloli a shirye-shiryenta sakamakon ɓarkewar cutar Ebola a ƙasarta.
DR Congo ta nuna kwarewa a wasanta na farko, inda ta yi kunnen doki 1-1 da kasar Portugal. Sai dai ta sha kashi a hannun Colombia a wasa na biyu.
Ta yi nasarar dole Uzbekistan da ci 3-1 don tsallakewa zuwa zagayen 'yan 32. A wasan da ta buga da Ingila, DR Congo ce ta fara zura ƙwallo kuma ta riƙe jagoranci har zuwa minti na 75, a cewar rahoton Sky Sports.
Sai dai Harry Kane ya ci ƙwallaye biyu da suka fitar da ita daga gasar. Duk da haka, ƙungiyar ta bar gasar da mutuncinta, saboda irin bajintar da ta nuna.
4. Masar
Matsayi: Zagayen 'yan 16

Source: Getty Images
Masar ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da suka fi taka rawar gani a gasar, bayan ta kammala wasannin rukuni a matsayi na biyu tare da samun tikitin zuwa zagayen 'yan 16.
Nasarar da ta samu kan New Zealand da ci 3-1 ta fito da bajintar ta, bayan ta yi kunnen doki da Belgium da Iran. Daga bisani ta doke Australia a bugun daga kai sai mai tsaron raga domin samun gurbi a zagayen 'yan 16.
A karawarta da Argentina, Masar ta kusa kafa babban tarihi, domin ta ci kwallaye biyu har zuwa kusa da ƙarshen wasan, kafin zakarun duniyar sun sauya komai, inda suka juya wasan suka yi nasara da ci 3-2.
5. Ghana
Matsayi: Zagayen 'yan 32

Source: Getty Images
Ghana ta shiga gasar ne ƙarƙashin sabon koci, Carlos Queiroz, wanda aka naɗa watanni kaɗan kafin fara Kofin Duniya.
Da aka fara gasar, Ghana ta doke Panama, sannan ta yi kunnen doki da Ingila. Sai dai rashin nasarar da ta yi a wasanta da Croatia, wanda aka tashi 2-1 ya sa ta kammala rukunin a matsayi na uku.
A zagayen 'yan 32, Ghana ta kara da Colombia, amma ta kasa nuna ƙwazon da ake bukata, kuma ba ta yi wa 'yan Kudancin Amurka wata babbar barazana ba kafin ta yi bankwana da gasar.
6. Ivory Coast
Matsayi: Zagayen 'yan 32
Ivory Coast ta nuna ƙwazo musamman a wasannin rukuni, inda ta samu nasara kan Ecuador da Curacao, yayin da ta sha kashi da ƙyar a hannun Jamus, lamarin da ya nuna cewa tana iya gogayya da manyan ƙasashe.
Sai dai Ivory Coast ta fuskanci ƙalubale lokacin da ta kara da Norway a zagayen 'yan 32, domin ta nuna juriya sosai, har wasan ya kasance 1-1 zuwa mintuna biyar na ƙarshe.
A ƙarshe, fitaccen ɗan wasan Norway Erling Haaland ya ci ƙwallar da ta ba ƙasarsa nasara, inda ya kawo ƙarshen wasan Ivory Coast a gasar.
7. Morocco
Matsayi: Zagayen daf da na ƙarshe

Source: Getty Images
Morocco ta kammala wasannin rukuni da maki bakwai, bayan ta yi kunnen doki da Brazil tare da samun nasara a kan Haiti da Scotland. Wannan sakamako ya ba ta damar tsallakewa cikin kwanciyar hankali zuwa zagayen 'yan 32.
A zagayen farko na wasannin fitar da gwani, Morocco ta doke Netherlands ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron raga. Daga nan kuma ta fitar da Canada cikin wasa da ta fi ƙarfin abokiyar karawarta, lamarin da ya tabbatar da cewa tana cikin manyan ƙungiyoyin gasar.
Sai dai tafiyarta ta zo ƙarshe a hannun Faransa a wasan daf da na ƙarshe, kamar yadda rahoton Aljazeera ya nuna.
Ganin cewa Morocco tana matsayi na bakwai a jadawalin FIFA, isa wannan mataki na gasar ya kasance mafi ƙarancin abin da ake tsammani daga gare ta, kuma rashin kai wasan kusa da na ƙarshe ya bar ɗan takaici a zukatan magoya bayanta.
8. Senegal
Matsayi: Zagayen 'yan 32

Source: Getty Images
Tun kafin fara gasar, Senegal ta shiga cikin matsaloli da suka haɗa da rashin jituwar wasu 'yan wasa da kuma batun kocin ƙungiyar wanda ya shiga gasar ba tare da sabunta kwantiraginsa ba, in ji rahoton Aljazeera.
Ba abin mamaki ba ne lokacin da Senegal ta sha kashi a wasanninta biyu na farko a hannun Faransa da Norway, duk da irin ƙwararrun 'yan wasan da take da su.
Sai dai daga baya ta farfaɗo sosai inda ta lallasa Iraq da ci 5-0, abin da ya ba ta damar tsallakewa zuwa zagayen 'yan 32 a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun ƙasashen da suka zo na uku.
A karawarta da Belgium, Senegal ta yi abin da ba a yi tsammani ba lokacin da ta ci ƙwallaye biyu, har zuwa saura mintuna biyar a tashi wasan.
Sai dai komai ya sauya cikin kankanin lokaci, Belgium ta rama ƙwallaye biyu, ta kai wasan ƙarin lokaci, sannan ta samu bugun fenariti a minti na 125, wanda ya tabbatar da nasararta da ci 3-2.
9. Afirka ta Kudu
Matsayi: Zagayen 'yan 32
Afirka ta Kudu ta rubuta sabon tarihi a gasar Kofin Duniya ta 2026 bayan ta kai zagayen 'yan 32 a karon farko tun bayan fara halartar gasar, kamar yadda shafin Live Score ya ruwaito.
Farkon gasar bai yi wa Bafana Bafana daɗi ba, domin Mexico ta doke ta da ci 2-0 cikin wasan da ta nuna rauni sosai. Sai dai ƙungiyar ta dawo da ƙarfi a wasanninta na gaba.
Ta fara da kunnen doki da Jamhuriyar Czech, sannan ta samu muhimmiyar nasara da ci 1-0 a kan Koriya ta Kudu, wanda ya tabbatar mata da tikitin zuwa zagayen 'yan 32.
Duk da rashin nasarar da ta yi da ci 1-0 a hannun Canada, 'yan wasa da magoya baya sun bar gasar cikin farin ciki saboda sabon tarihin da ƙungiyar ta kafa.
10. Tunisia
Matsayi: Matakin rukuni

Source: Getty Images
Tunisia ita ce kaɗai daga cikin ƙasashen Afirka 10 da ta kasa tsallakewa daga matakin rukuni. Ƙungiyar ta sha manyan kaye a hannun Sweden da ci 5-1, Japan da ci 4-0, sannan Netherlands ta doke ta da ci 3-1.
Hukumar ƙwallon ƙafar Tunisia ta kori koci Sabri Lamouchi bayan kashin da Sweden ta yi mata, duk da cewa ƙungiyar ta riga ta shiga gasar ne bayan ta sha kashi 5-0 a hannun Belgium a wasan sada zumunta na ƙarshe.
Kasashen da suka fi cin kwallaye
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Brazil da Jamus sun ci gaba da zama ƙasashen da suka fi cin ƙwallaye a tarihin gasar cin Kofin Duniya ta FIFA.
Argentina da Faransa na ci gaba da matsowa gaba, yayin da suke cikin ƙasashen da suka kai wasan kusa da na ƙarshe a 2026.
A hannu daya kuma, Spain da Ingila na da damar ƙara yawan ƙwallayensu yayin da gasar cin Kofin Duniya ta 2026 ke dab da ƙarewa.
Asali: Legit.ng






