KAI TSAYE: Yadda Wasan Portugal da Spain Yake Gudana a Gasar Kofin Duniya, 2026
Spain ta yi sauyi: Fabián Ruiz ya shiga
Kocin Spain ya yi sauyi a tsakiya, inda Fabián Ruiz ya maye gurbin Pedri domin ƙara ƙarfi da sababbin dabaru a mintunan ƙarshe na wasan.
Minti: 85
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Portugal ta yi sauye-sauye 2
Kocin Portugal ya sake yin sauye-sauye biyu domin ƙara kuzari a ƙarshen wasa. Francisco Conceição ya maye gurbin Pedro Neto, yayin da Bernardo Silva ya shiga a madadin Vitinha.
Minti: 83
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Spain na ƙara matsa wa Portugal lamba
Rúben Dias ya yi gagarumar ceto ta kwance ya tare harbin Dani Olmo a cikin akwatin fanareti. Spain ce ke mamaye wasan a wannan lokaci.
Minti: 80
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Yamal ya kusa jefa Spain a gaba
Lamine Yamal ya samu bugun daga kai sai masu tsaron gida a gefen akwatin fanareti kuma shi ne ya buga. Karfin harbinsa ya tilasta Diogo Costa tura ƙwallon sama da raga.
Minti: 74
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Wani sauyi a Portugal: Dalot ya maye gurbin Cancelo
Portugal ta sake yin sauyi, inda Diogo Dalot ya shiga fili a madadin João Cancelo domin ƙara ƙarfi a bangaren tsaro da kai hari.
Minti: 71
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Portugal ta yi sauyi: Leão ya shiga
Kocin Portugal ya yi sauyi, inda Rafael Leão ya maye gurbin João Félix domin ƙara wa ƙungiyar kuzari a bangaren kai hari.
Minti: 71
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Har yanzu ana jiran wanda zai fara kuskure
Har yanzu babu wani koci da ya yi sauyi na dabara, yayin da wasan ke ci gaba da zama babu ƙwallo. Ana sa ran sauye-sauye za su iya sauya alkiblar wasan.
Minti: 66
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Pedri ya yi harbi sama da raga
Pedri ya samu damar harbi bayan Dani Olmo ya ƙwace ƙwallo a bakin akwatin bugun fanareti, amma ƙwallon ta wuce saman ragar Portugal ba tare da ta dami mai tsaron gida ba.
Minti: 62
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Har yanzu babu wanda ya karya canjaras
Har yanzu duka ƙasashen na fama wajen samun hanyar zura ƙwallo. João Félix ya daga ƙwallo zuwa Cristiano Ronaldo, amma kyaftin ɗin Portugal ya kasa yin ingantaccen harbi.
Minti: 60
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Raunin Mendes ya rage wa Portugal ƙarfi
Fitar Nuno Mendes saboda rauni ta zama babbar illa ga Portugal, domin yana daga cikin 'yan wasan da suka fi kawo barazana a kai hare-hare.
Minti: 57
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Canji a Portugal: Semedo ya maye gurbin Mendes
Kocin Portugal ya yi sauyi na farko, inda Nélson Semedo ya shiga wasan a madadin Nuno Mendes, wanda ya fita saboda rauni.
Minti: 56
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
An dawo daga hutun rabin lokaci
An dawo daga hutun rabin lokaci, inda Portugal ta fara da ƙwallo yayin da wasa ya ci gaba a filin wasa na Dallas.
Minti: 46
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
An tafi hutun rabin lokaci
An kawo ƙarshen rabin farko ba tare da an zura ƙwallo ba. Duk da cewa Spain ta fi mallakar wasa a wasu lokuta, Portugal ta tsaya tsayin daka, inda aka tafi hutun rabin lokaci da canjaras.
Minti: Hutu (Rabin lokaci)
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Spain na ƙara matsa lamba
Spain na ci gaba da kai hare-hare yayin da rabin farko ke gab da ƙarewa. Lamine Yamal ya yi harbi daga kusa da raga, amma ya fita waje, sannan aka daga tuta saboda ya yi offside.
Minti: 45+3
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
An ƙara mintuna 6
Alƙalin wasa ya ƙara mintuna shida a ƙarshen rabin farko. A farkon ƙarin lokacin, Rodri ya yi harbi daga bakin akwatin bugun fanareti, amma ƙwallon ta wuce saman raga.
Minti: 45+1
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Félix ya dakatar da Yamal
João Félix ya yi kokarin dawowa baya cikin lokaci, inda ya ƙwace wa Lamine Yamal ƙwallo cikin tsafta, tare da dakile wani hari mai haɗari na Spain.
Minti: 44
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Mendes ya buga ƙwallo ta bugi sandar raga
Portugal ta kusa samun ƙwallo bayan Nuno Mendes ya harba ƙwallo mai ƙarfi daga bakin akwatin bugun fanareti, wadda ta ɗan sauya hanya kafin ta bugi sandar ragar Spain.
Minti: 42
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Ronaldo ya kusa zura kwallo
Portugal ta samu babbar dama bayan João Félix ya mayar da ƙwallo cikin akwati daga gefe. Cristiano Ronaldo ya yi ƙoƙarin karkatar da ita zuwa raga, amma mai tsaron Spain, Unai Simón, ya dawo da sauri ya kama ƙwallon.
Minti: 39
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Spain ta samu bugun kusurwa
Spain ta buga bugun kusurwa a takaice, sannan ta rika musayar ƙwallo a bakin akwatin bugun fanareti. Daga bisani aka tura ƙwallo cikin akwatin, Costa ya kabe ta kafin alƙali ya daga tuta, yana nuna an yi offside.
Minti: 32
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Spain na ƙara matsa lamba
Spain na ci gaba da ƙara kai hare-hare. Dani Olmo ya yi ƙoƙarin cusa wa Lamine Yamal ƙwallo, amma Nuno Mendes ya datse ta a kan lokaci.
Minti: 30
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
An koma wasa
An dawo daga hutun shan ruwa, inda 'yan wasan Portugal da Spain suka ci gaba da fafatawa domin neman gurbin zuwa zagayen kwata fainal.
Minti: 27
Sakamako: Portugal 0-0 Spain
An Dakatar da Wasa na Ɗan Lokaci
An dakatar da wasan na ɗan lokaci domin 'yan wasan su sha ruwa bayan mintuna 23 da aka buga. Har yanzu babu wata ƙungiya da ta samu nasarar zura ƙwallo.
⏱️ Minti: 23' 📊 Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Wasan na tafiya cikin ƙayatarwa
Ana fafata wasa mai zafi tsakanin Portugal da Spain, inda kowacce ƙungiya ke riƙe ƙwallo cikin natsuwa tare da ƙoƙarin ƙirƙirar damar cin ƙwallo.
Spain ce ta samu damar da ta fi hatsari kawo yanzu, amma ba ta mamaye wasan gaba ɗaya ba.
⏱ Minti: 21 📊 Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Spain ta matsa lamba
Spain ta kusa farke ƙwallo bayan ta kai hare-hare masu haɗari. Diogo Costa ya hana Yamal zura ƙwallo, sannan ya sake ceto wata ƙwallo mai ƙarfi da Oyarzabal ya buga.
⏱️ Minti: 18 📊 Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Ronaldo ya tilasta an ba Portugal bugun kusurwa
Cristiano Ronaldo ya kai farmaki bayan ya karɓi ƙwallo a gefen dama, inda ya kutsa cikin akwatin bugun daga kai sai mai tsaron Spain, Unai Simón, ya hana shi cin ƙwallo. Sai dai bugun kusurwar da aka samu bai haifar da wata barazana ba.
⏱ Minti: 13' 📊 Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Babbar dama ta Spain ta salwanta
Oyarzabal ya sake samun babbar dama bayan kyakkyawan fasin daga Olmo, amma harbinsa daga cikin akwatin bugun fenariti ya wuce gefen raga.
Minti: 10 - Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Cancelo ya gwada sa'a
João Cancelo ya harba ƙwallo daga wajen akwatin bugun fenariti bayan Portugal ta kai hari, amma ƙwallon ta wuce saman raga ba tare da ta dami mai tsaron Spain ba.
Minti: 8' Sakamako: Portugal 0-0 Spain
Spain ta fara gwada Costa
Spain ta fara nuna sa'arta bayan ta kwace ƙwallo a tsakiyar fili, inda Mikel Oyarzabal ya kutsa da gudu kafin ya harba daga wajen akwatin bugun fanareti. Sai dai mai tsaron ragar Portugal ya kama ƙwallon cikin sauƙi.
Sakamako: Portugal 0-0 Spain