Majalisar Shari'ar Musulunci Ta Najeriya Ta Hango Matsala a Shirin Kafa Yan Sandan Jihohi
- Majalisar Koli ta Shari'ar Musulunci a Najeriya (SCSN) ta bada shawara kan gyaran kundin tsarin mulki game da kafa 'yan sandan jihohi
- Ta ce matsalar tsaro ba za ta kare da kafa 'yan sandan jihohi kadai ba, tana mai cewa ya kamata a yi dogon nazari kan lamarin
- Majalisar ta bukaci a fara gyara da karfafa hukumomin tsaro da ake da su, tana mai gargadin kada a mayar da 'yan sandan jihohi kayan danniya na siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Koli ta Shari'a a Najeriya (SCSN) ta ja hankalin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Majalisar Tarayya, gwamnatocin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki kan kafa yan sandan jihohi.
Majalisar ta bukaci su kammala cikakkiyar tuntuba da 'yan Najeriya tare da magance damuwar jama'a kafin ci gaba da gyaran kundin tsarin mulki da zai ba da damar kafa 'yan sandan jihohi.

Source: Facebook
Rahoton Leadership ya ce Majalisar ta gargadi gwamnati da Majalisar Tarayya da su guji gaggauta amincewa da wannan gyara, tana mai cewa batun na da matukar tasiri ga adalci, hadin kan kasa da makomar Najeriya.
SCSN ta ce matsalar tsaro ta yi kamari
A wata sanarwa da Sakatare Janar na majalisar, Nafiu Baba Ahmad, ya fitar, SCSN ta ce ta na bibiyar muhawarar da ake yi da kuma matakan da ake dauka kan batun kafa 'yan sandan jihohi.
Majalisar ta amince cewa Najeriya na fuskantar daya daga cikin mafi munin matsalolin tsaro a tarihinta, inda aka rasa dubban rayuka, miliyoyin mutane suka rasa matsugunansu, yayin da noma, kasuwanci da hanyoyin samun abinci suka lalace.
Sai dai ta jaddada cewa duk da bukatar samar da mafita, bai kamata a dauki kafa 'yan sandan jihohi a matsayin mafita ta gaggawa ga matsalar tsaro ba, cewar rahoton Tribune Nigeria.
Ta bukaci a gyara hukumomin tsaro
SSCN ta bukaci gwamnati ta mayar da hankali kan gyara da karfafa hukumomin tsaro da ake da su ta hanyar samar da karin kudade, daukar karin jami'ai, amfani da fasahar zamani, Inganta tattara bayanan sirri da karfafa tsaron iyakoki
Majlisar Shari'a ta kuma nuna damuwa kan abin da ta kira gaggawar da ake yi wajen gyaran kundin tsarin mulki kan batun kirkiro yan sandan jihohi.

Source: Twitter
Ta kuma yi gargadi cewa kada tsarin 'yan sandan jihohi ya zama hanyar amfani da jami'an tsaro wajen tsoratar da abokan adawa ko nuna bambanci.
Ta ce saboda bambancin addini, kabila da siyasa da ke Najeriya, dole ne duk wani tsarin tsaro ya tabbatar da kariya da adalci ga kowane dan kasa ba tare da nuna bambanci ba.
Fadar shugaban kasa ta yi bayani
A wani rahoton, kun ji cewa Fadar Shugaban Kasa a Najeriya ta yi karin haske game da shirin kafa ƴan sanda a Najeriya.
Fadar ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a shirin kafa sabuwar rundunar yan sandan, wacce ta ce an dade ana aiki a kai domin magance matsalar tsaro.
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan bayan wani taron tattaunawa kan batun ‘yan sandan jihohi da Fadar Shugaban Kasa ta shirya a Abuja.
Asali: Legit.ng

