Albashin N150000 da Wasu Abubuwa 9 game da Shirin The Power Force na Tinubu

Albashin N150000 da Wasu Abubuwa 9 game da Shirin The Power Force na Tinubu

Abuja – Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin 'The Power Force' domin horar da matasa 5,000 kan girka mitocin lantarki masu amfani da fasahar zamani a ƙarƙashin Shirin Shugaban Ƙasa na Samar da Mitoci (PMI).

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Shirin na daga cikin manufofin gwamnatin shugaban ƙasa na samar da ayyukan yi ga matasa, rage matsalar rashin mitoci da kuma kawo ƙarshen tsarin kiyasci a lissafin kuɗin lantarki, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin The Power Force na horar da matasa 5,000
Shugaba Bola Tinubu ya na sanya hannu kan wata takarda da wani matashi yana danna waya yana murmushi. Hoto: @officialABAT/X, MStudioImages/Getty Images
Source: Getty Images

Abubuwan sani game da The Power Force

Ga wasu abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da shirin kamar yadda aka walla a shafin X na fadar shugaban kasa:

1. Za a horas da matasa 5,000

Shirin The Power Force zai bai wa matasa 5,000 horo kan yadda ake girka mitocin lantarki masu amfani da fasahar zamani, kafin a tura su aiki a sassa daban-daban na ƙasar.

Kara karanta wannan

Tinubu zai dauki matasa 5,000 domin ba su horo su samu sana'a

2. Manufar rage gibin mitocin lantarki

A halin yanzu miliyoyin masu amfani da wutar lantarki ba su da mitoci, abin da ke jefa su cikin biyan kuɗin lantarki bisa ƙiyasin kamfanonin rarraba wuta. Shirin zai samar da ƙwararrun ma'aikata domin hanzarta girka mitoci a faɗin ƙasar.

3. Horon kyauta ne gaba ɗaya

Ba za a karɓi ko sisin kwabo daga waɗanda za a zaɓa ba. Gwamnati ce za ta ɗauki nauyin horon domin bai wa matasa damar koyon sana'ar fasaha ba tare da wata matsala ba.

4. Ba sai kana da digiri ba

Duk ɗan Najeriya da ya kammala karatun sakandare kuma ya cika sharuddan shiga zai iya neman shiga shirin, ba tare da la'akari da ko ya yi karatun jami'a ko a'a ba.

5. Albashin ₦90,000 zuwa ₦150,000

Gwamnati ta bayyana cewa shirin ba horo kaɗai zai bayar ba, domin waɗanda suka kammala za su samu damar aiki tare da samun albashi tsakanin Naira 90,000 zuwa Naira 150,000 a kowane wata.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun bindige yaro dan shekara 10, sun sace matan aure a Sokoto

6. Za a koyar da yadda ake girka mitoci

Masu horon za su samu ilimi da ƙwarewa kan:

  • Girka mitocin lantarki na zamani
  • Ka'idojin tsaron lantarki
  • Hanyoyin gudanar da aikin fasaha
  • Dabarun aikin da ake buƙata domin fara aiki a fannin

7. Za a bada takardar shaidar ƙwarewa

Bayan kammala horon, mahalarta za su samu takardar shaidar ƙwarewa da za ta taimaka musu wajen samun damar aiki a fannin makamashi da lantarki.

8. An ware gurbi ga 'yan NYSC

Shirin ya tanadi gurabe na musamman ga mambobin Hukumar Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) domin su haɗa hidimar ƙasa da koyon sana'a mai amfani.

Fadar shugaban kasa ta ce shirin zai rika samarwa matasan albashin N90,000 zuwa N150,000.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na jawabi a wani taro a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

9. Kawo ƙarshen 'kiyascin kudin wuta'

Gwamnati ta ce yawaitar mitoci zai tabbatar da cewa masu amfani da lantarki suna biyan kuɗin wutar da suka sha kawai, tare da ƙara gaskiya a harkar rarraba wutar lantarki da jawo sababbin zuba jari a fannin.

10. Lokacin fara neman shirin

Yayin da za a fara karɓar buƙatun shiga cikin shirin ranar Asabar, 4 ga Yulin 2026, matasan da suka cika sharuddan shiga za su iya neman gurbi ta shafin yanar gizon shirin shugaban kasa na samar da mitoci (PMI) da ke: pmi.naptin.gov.ng.

Kara karanta wannan

Minista ka iya rasa kujerarsa, an kirayi Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci

Shirin The Power Force na da manufar haɗa manyan burin gwamnati guda biyu wuri guda: samar da ayyukan yi ga matasa da kuma kawo ƙarshen matsalar ƙarancin mitocin lantarki a Najeriya.

Karanta sanarwar a nan kasa:

Gwamnatin Tinubu za ta dauki matasa aiki

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Bola Tinubu ta bude shafin daukar matasa aiki a karkashin shirin kiwon lafiya na NHFP daga dukkanin jihohin Najeriya.

Gwamnatin ta sanar da cewa za ta ba wadanda aka dauka aikin alawus mai gwabi da kayan aiki don kawo sauyi a tsarin kiwon lafiya.

Legit Hausa ta yi bayani dalla dalla yadda matasa 'yan kasa da shekaru 35 za su iya neman wannan aikin da takardun da ake bukata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com