APC: Kwankwaso Ya Kwashe Mutanen Abba Kabir da Ganduje zuwa NDC
- Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi wasu masu sauya sheƙa daga APC
- Rabiu Kwankwaso ya tabbatar musu da cewa za su samu adalci da kuma matsayi mai kyau a cikin jam'iyyar bayan komawarsu
- Karɓar masu sauya sheƙar na zuwa ne yayin da jam'iyyar adawa ta NDC ke ƙoƙarin faɗaɗa tasirinta a Kano gabanin zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi wasu jiga-jigan masu sauya sheƙa daga jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Madobi da ke jihar Kano.
Kwankwaso ya bayyana farin cikinsa kan sauya shekar tasu, yana mai cewa jam'iyyar NDC za ta ba su cikakkiyar dama da kuma matsayi mai kyau a cikinta.

Source: Facebook
Rahoto ya nuna cewa tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi.
Abin da Kwankwaso ya faɗa
Kwankwaso ya ce ya yi matuƙar farin ciki da karɓar waɗanda suka fice daga APC domin shiga jam'iyyar NDC.
Ya ce:
"Na yi matuƙar farin ciki da karɓar wasu masu sauya sheƙa daga ƙaramar hukumar Madobi waɗanda suka bar APC suka koma jam'iyyar NDC."
Punch ta wallafa cewa ya ƙara da cewa:
"Na yi masu maraba cikin jam'iyyarmu tare da tabbatar masu cewa za su samu adalci da matsayi mai kyau a cikin NDC."
Ana ganin NDC na ƙara ƙarfi a Kano
Hotunan taron sun nuna Kwankwaso cikin farar tufa da kuma jar hularsa ta Kwankwasiyya yana jawabi ga dubban magoya baya tare da ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya na NDC, Nasiru Gawuna.
Haka kuma, an ga dimbin magoya bayan jam'iyyar NDC sanye da jajayen hulunan Kwankwasiyya suna tafi da murna yayin taron.
Mutane da dama sun bayyana cewa taron ya nuna har yanzu Kwankwaso na da ƙwararan magoya baya a Kano duk da sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu daga cikin kusoshinsa zuwa APC.

Source: Facebook
Siyasar Kano na cigaba da daukar hankali, musamman lura da yadda ake hasashen yadda za a fafata tsakanin mataimakin dan takarar shugaban kasa na NDC da masu kokarin samawa Tinubu kuri'u.
Rabiu Kwankwaso zai yi kokarin ganin ya samawa NDC kuri'u masu yawa yayin da Abba Kabir Yusuf za su yi kokarin samawa APC kuri'u.
Batn rasuwar kosan waka
A wani labarin, mun ruwaito cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana alhininsa kan rasuwar fitaccen mawaƙi Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waka.
Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce gudunmawar Kosan Waka wajen yaɗa manufofin tafiyar Kwankwasiyya ba za ta taɓa gushewa ba a tarihi.
Ya yi addu'ar Allah ya jikansa da rahama, ya ba shi Aljannatul Firdausi tare da jajanta wa iyalansa da abokansa kan wannan babban rashi.
Asali: Legit.ng

