An yi wa Amurka Kaca Kaca a Kofin Duniya duk da Shiga da Fitar Trump a Boye

An yi wa Amurka Kaca Kaca a Kofin Duniya duk da Shiga da Fitar Trump a Boye

  • Kasar Belgium ta doke 'yan wasan Amurka da ci 4-1, inda ta fitar da ita daga gasar cin kofin Duniya a zagayen rukuni na 16
  • Hukuncin hukumar FIFA na barin Folarin Balogun ya buga wasa duk da jan katin da ya samu ya haifar da ce-ce-ku-ce a duniya
  • Koci Mauricio Pochettino ya ce batun Balogun bai jawo rashin nasarar Amurka ba, amma ya soki yadda aka siyasantar da batun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Burin Amurka na lashe kofin duniya karo na farko ya zo karshe cikin yanayi mai cike da rudani a ranar Talata, bayan ta sha kashi a hannun Belgium.

Amurka ta sha kashi da ci 4-1, wanda shi ne mafi muni tun shekarar 1990. Yanayin annashuwa da ya kasance a wasanninta na baya ya dusashe tun kafin ƙarshen wasan.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Ronaldo ya faɗi lokacin da zai yi ritaya daga bugawa Portugal ƙwallo

'Yan wasan Amurka a filin wasa
'Yan kwallon Amurka bayan an kwarfe su a kofin duniya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

BBC ta wallafa cewa bayan zura ƙwallo ta huɗu da Belgium ta yi, dimbin magoya bayan Amurka suka fara ficewa daga Filin Wasan Seattle.

Trump ya jawo rudani

Fitar Amurka daga gasar a zagayen 'yan wasa 16, duk da kasancewarta ɗaya daga cikin ƙasashen da suka karɓi baƙuncin gasar, ya biyo bayan wasu kwanaki masu cike da ce-ce-ku-ce.

Labarai sun fi mayar da hankali kan matakin da FIFA ta ɗauka na dakatar da hukuncin jan kati da aka bai wa Folarin Balogun a wasan baya, lamarin da ya ba shi damar buga wasan da aka doke Amurka.

Hanyar da Amurka ta bi zuwa wannan mataki ta jawo hankalin jama'a sosai, amma rikicin Balogun ya rage wannan farin ciki, abin da 'yan wasan Belgium ma suka lura da shi kafin wasan.

Ɗan wasan baya na Belgium, Timothy Castagne, ya ce:

"Abin farin ciki ne ganin duniya tana bayanmu wajen adawa da Amurka."

Kara karanta wannan

Elon Musk ya taba Trump, ya ce Afirka ta tsira da Amurka ta bar ba ta agaji

Balogun kuwa ya ce bai yi mamakin yadda batun ya zama abin cece-kuce ba.

Ya ce:

"Na amince da hukuncin lokacin da aka ba ni jan kati, sannan na sake amincewa lokacin da aka sanar da ni cewa zan iya buga wasan.
"Ba ni da wani abu da zan ƙara cewa kan wannan batu."

Lamarin har ya kai ga siyasar Amurka, inda New York Times ta ce Shugaba Donald Trump ya ce ya buƙaci FIFA ta sake duba hukuncin saboda a ganinsa ba laifi ba ne.

Folarin Bologun a filin wasa
Folarin Bologun da ake ce-ce-ku-ce a kan shi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Belogun bai ceci Amurka ba

Balogun, wanda ya ci ƙwallaye uku a gasar cin kofin duniya, ya fara wasan da Belgium amma bai taka rawar gani ba.

Da aka tambayi kocin Amurka bayan wasan ko ce-ce-ku-cen da aka yi kan Balogun ya shafi ƙungiyarsa, sai ya ce:

"Bai shafi yadda muka taka leda ba.
"Na ji takaici. Sun saka siyasa da son zuciya cikin wannan batu,"

An cire Portugal a kofin duniya

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sifaniya ta kai wasan daf da na kusa da na ƙarshe na gasar kofin duniya ta 2026 bayan ta doke Portugal da ci 1-0.

Kara karanta wannan

Trump ya sake zama kan yiwuwar koma wa yaƙi da Iran

Bayan mintuna 90 na wasan ba tare da an zura ƙwallo ba, ɗan wasan da ya shigo daga benci, Merino, ya ci wa Sifaniya ƙwallo a ƙarshen wasan a birnin Dallas.

Wannan rashin nasara ya kawo ƙarshen burin Cristiano Ronaldo na lashe kofin duniya, wanda wannan ita ce gasarsa ta ƙarshe, inda yake fatan ɗaga kofin a karon farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng