Martanin Gwamnatin Tarayya Bayan Kisan ’Yan Najeriya 2 a Afirka Ta Kudu
- Gwamnatin Tarayya ta yi Allah wadai da kisan wasu 'yan Najeriya biyu a Afirka ta Kudu, tare da neman a gudanar da bincike
- Kasar ta nuna damuwa kan karuwar hare-haren ƙyamar baƙi, tana gargadin cewa ci gaba da hakan na iya lalata dangantakar Najeriya da Afirka ta Kudu
- Najeriya ta bukaci 'yan kasarta su kwantar da hankali, su guji ɗaukar doka a hannu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta yi martani bayan kisan yan Najeriya da aka yi a kasar Afirka ta Kudu yayin da ake rikicin kin jinin baki.
Kasar ta yi Allah wadai da kisan wasu 'yan Najeriya biyu a Afirka ta Kudu, tare da buƙatar hukumomin ƙasar su gudanar da bincike cikin gaggawa tare da hukunta masu hannu a laifin.

Source: Twitter
Hakan na cikin sanarwar da mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ya fitar, cewar Punch.
Sunayen wadanda aka kashe a Afirka ta Kudu
Sanarwar ta bayyana sunayen mamatan da Emeka Charles Iroegbu da Musa Yunana Joe, wanda aka fi sani da Big Joe.
Ma'aikatar ta ce ana zargin jami'an 'yan sandan Tshwane Metro sun kashe Iroegbu a ranar 28 ga Yunin 2026 a Sunnyside da ke Pretoria yayin wata tambayoyi mai cike da zalunci.
Ta ƙara da cewa ana kuma zargin jami'an guda huɗu da kashe wani ɗan Najeriya, Nnaemeka Mathew Andrew Ekpenyong, a ranar 20 ga Afrilu, 2026, ba tare da gurfanar da kowa ba.
Game da Musa Yunana Joe, gwamnatin ta ce an kashe shi ne a gaban shagonsa da ke Witbank a Mpumalanga ranar 28 ga Yuni, inda har yanzu ba a gano waɗanda suka aikata laifin ba.

Source: Facebook
Shawarar gwamnatin Najeriya ga Afirka ta Kudu

Kara karanta wannan
Babbar magana: Kotu ta ƙwace Naira miliyan 150 na wani 'dan Majalisar tarayya a Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta ce waɗannan hare-haren sun faru ne a daidai lokacin da ake fama da hare-haren ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu, abin da ya ƙara jefa rayuwar 'yan Najeriya cikin haɗari.
Ta jaddada cewa ko da akwai zargi a kan wani mutum, dole ne a bi hanyoyin doka tare da ba shi damar kare kansa a gaban kotu maimakon kashe shi ba bisa ƙa'ida ba.
Har ila yau, ta kuma roƙi 'yan Najeriya da ke gida kada su ɗauki fansa, tana mai cewa za ta ci gaba da amfani da tattaunawa da hanyoyin diflomasiyya wajen warware matsalar.
Ma'aikatar ta bayyana cewa ana ci gaba da kwashe 'yan Najeriya da suka yi rajista daga Afirka ta Kudu, tare da jaddada cewa gwamnatin ƙasar na da alhakin kare rayuka da dukiyoyin dukkan baƙi.
Yan Najeriya sun dauki makamai a Afirka ta Kudu
A baya, mun ji cewa wasu 'yan Najeriya sun shirya kare kansu a kasar Afirka ta Kudu bayan wa'adin 30 ga Yunin shekarar 2026 da aka ba baki.
Kungiyoyin masu adawa da baƙi sun nemi a kori baki ɗaya baƙin da ke ƙasar, yayin da aka kashe wasu 'yan ƙasashen Afirka a hare-haren.
Gwamnatin Najeriya ta sake yin Allah wadai da hare-haren, tare da buƙatar hukumomin Afirka ta Kudu su tabbatar da tsaron 'yan kassarta.
Asali: Legit.ng
